Matatar mai ta Dangote ta fayyace cewa ba ta karɓi wani kuɗi daga Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN) ba domin sayen manta da aka tace.
Matatar ta ce duk da cewa ana ci gaba da tattaunawa da ƙungiyar ta IPMAN, amma abin takaici ne a ce su (Mambobin IPMAN) suna fuskantar matsalar lodin man da aka tace daga matatarmu, domin a halin yanzu ba mu da wata hulɗar kasuwanci da su. Saboda haka, ba za a iya ɗaukar alhakin duk wani kuɗin da aka yi wa wasu ƙungiyoyi ba.
Sanarwar da matatar ta fitar ta hannun Babban Jami’in Yaɗa Labarunta, Mista Anthony Chiejina ta qara da cewa, “an biya kuɗin da aka ambata ta hannun Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL), ba mu ba. Haka zalika, NNPCL bai yarda ko ba mu izini mu saki man fetur ga ƙungiyar IPMAN ba.
“Muna so mu jaddada cewa za mu iya biyan buƙatun al’umma na duk wani nau’in man fetur da suka haɗa da fetur, dizal, da man jiragen sama. A halin yanzu, muna iya lodin manyan motoci 2,900 a kowace rana, haka kuma muna dakon man fetur ta ruwa. Muna ba IPMAN shawara da ta yi rajista da mu kuma ta biya kai tsaye, saboda muna da isassun albarkatun man fetur don biyan buƙatun mambobinsu.
“Bugu da ƙari kuma, muna ganin yana da kyau duk masu ruwa da tsaki su guji furta kalamai marasa tushe a kafafen yaɗa labarai, domin hakan na iya kawo cikas ga ƙoƙarin sake farfaɗo da tattalin arzikin da Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke yi. Gudanar da kasuwanci ta maramtacciyar hanya ba shi da amfani kuma rashin kishin ƙasa ne.
“Muna ƙarfafa duk masu ruwa da tsaki su ba da haɗin kai tare da bin shawarwarin Shugaba Tinubu, da inganta tsarin haɗin kai, maimakon shiga cikin rikice-rikicen kafofin watsa labaru da farfaganda mara amfani,” in ji Chiejina.