Connect with us

MANYAN LABARAI

Ba Mu Yi Nadamar Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba –Gwamnatin Zamfara

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin gwamna Bello Mohammed (Matawallen Maradun), ta ce ba ta yi nadamar matakin da ta dauka na yin sulhu da ‘yan bindigar da suka addabi jihar ba.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar, Zailani Bappa ya fitar yau Lahadi.

A cewarsa, sulhun shi ne hanyar da ta fi dacewa wajen kawo karshen hare-haren da ‘yan bindigar suka kwashe shekara da shekaru suna kai wa a jihar da ma wasu jihohin arewa maso yammacin Nijeriya.

‘Mun yi tattaunawar zaman lafiyar ne a matsayin hanyar gaskiya ta magance matsalolin jihar Zamfara kuma mun samu ci gaban da ba a yi tsammani ba a shekara daya da ta gabata.’ Inji Matawalle

Yaa kara da cewa dole dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiyar jihar su kasance masu gaskiya idan ana son dorewar zaman lafiya.

 

A kasance tare damu don samun cikakkun labarai…
Advertisement

labarai