Sabon dan wasan Real Madrid Kylian Mbappe ya ce ba dadin buga wasa da abin kariyar fuska, bayan da Faransa za ta fuskanci a Portugal a karawar zagaye na kusa da na kusa da na karshe a Euro 2024.
Dan wasan mai shekara 25 ya ji rauni a karan hanci a wasan farko a cikin rukuni da Faransa ta ci Austria 1-0 a gasar ta cin kofin Nahiyar Turai, kuma bai buga wasa na biyu ba da suka tashi ba ci da Netherlands, amma ya buga a fafatawa ta uku a cikin rukuni da suka tashi 1-1 da Poland kuma a wasan ne Mbappe ya buga da abin kariyar fuska, wanda ya ce bai samu sukuni ba.
- Kotu Ta Daure Uban Da Ya Dirka Wa ‘Yarsa Ciki A Bayelsa
- Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando
Mbappe ya sanar cewar kafin fuskantar Portugal yin wasa da abin kariyar fuska ba dadi saboda yana ta sauya kariyar fuskar, domin ina cin karo da wani abin da ya kamata a kara ko kuma a cire.
”Gaskiya da wahala, domin yana rage min gani, kuma gumi baya sauka daga goshi, har sai na cire kariyar fuska amma tun da ina iya cire fuskar kariyar ba wata matsala, kuma ba ni da wani zabi,” in ji dan wasan.
Idan Faransa ta doke tawagar kasar Portugal za ta fuskanci Sipaniya ko kuma mai masaukin baki Jamus kuma a wasan za a hadu tsakanin Ronaldo daga Portugal da Mbappe mai wakiltar Faransa.