Connect with us

LABARAI

Ba Ni Da Sauran Burin Siyasa Bayan 2023 – Masari

Published

on

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya shelanta cewa ba shi da sauran wani buri na siyasa a bayan shekarar 2023.

Gwamna Masari ya sake nanata cewa ba zai sake neman wani mukamin siyasa ba a bayan da ya riki mukamin gwamna har sau biyu.

Masari wanda ya yi wannan jawabin ga manema labarai a gidan gwamnatin Jihar da ke Katsina, ya ce ya gwammace ya bai wa matasa dama su ma su taka tasu rawar.

Masari ya ce domin a shekarar 2023 shekarunsa na haihuwa za su cika 73 kenan cif-cif.

Tsohon Kakakin majalisar wakilai ta kasan ya ce: “Ina bayyana matsayata a sarari ne, a bisa abin da nake shirya wa kaina.

“Ba ni da wani burin yin takarar wani mukami a bayan wannan da nake a kai a halin yanzun, duk da ko a baya can ban taba zaton zan shiga harkar siyasa ba, sam siyasa ba ta daga cikin abinda na ke tunani amma sai ga shi kaddara ta fado da ni a cikin harkokin siyasar.

“Ba ni na kawo kaina siyasa ba, kaddara ce ta kawo ni, ban ma taba tunanin zamana kwamishina zai kai ni ga shiga siyasa ba, domin in har da na san hakan, to kila da ba zan karbi mukamin kwamishinan ba, domin ba ni da tabbacin zan iya harkokin siyasa domin ni mai aikin sana’ar hannu ne ban taba zama wani shugaba ba har sai da na kai matakin shugaban, don haka a lokacin fatana ba shi ne na yi takarar wani mukami ba, ba kuma na je majalisar Dattawa ba. Don haka ba zan yi hakan ba, in Allah Ya so a shekarar 2023 Ina cika shekaru 73 da haihuwa cif-cif, a lokacin kuma ni na gama nawa takarar.
Advertisement

labarai