Yanzu haka ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi na ziyara a wasu kasashen Afirka, ziyarar dake zama al’adar shekaru 34 ke nan a jere da kowane ministan harkokin wajen Sin ke fara kaiwa wasu kasashen nahiyar ziyara a duk farkon kowace shekara.
Tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayani game da manufar kasar Sin ga nahiyar Afrika a Tanzania, wadda ta tsara makomar huldar kasashen Sin da Afrika a sabon zamani, wadda yanzu haka ta haifar da kawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin bangarorin biyu.
- Xi Ya Taya Felix Antoine Tshisekedi Murnar Lashe Zaben Shugaban Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo
- Shugaban Kasar Tunisiya Ya Gana Da Wang Yi
Ita dai wannan manufa da shugaba Xi Jinping ya gabatar, yayin ziyararsa ta farko da ya kai nahiyar Afrika, a matsayinsa na shugaban kasar Sin, a shekarar 2013 ta dogaro ne bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna,
Bisa wadannan tsare-tsare, kasashen Sin da Afrika sun dunkule waje guda, wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai daya, da nufin samar da dangantaka mai karfi da ba a taba ganin irinta ba, tsakanin kasar dake nahiyar Asia da kuma nahiyar Afrika, wadanda yawan al’ummarsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin daya bisa ukun al’ummar duniya baki daya.
Bayan wadannan shekaru, ana iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika a fannonin da suka hada da tattalin arziki,da ilimi, da cinikayya, da kayayyakin more rayuwa, da al’adu, da fannin noma,da raya masana’antu da ma kaiwa juna ziyara a bangaren manyan jami’ai da shugabannin sassan biyu.
Tarukan dandalin hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afrika FOCAC, da suka gudana a wurare da lokuta daban-daban, wani gagarumin ci gaba ne ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Wadanda ke aikewa da muhimmin sako ga al’ummomin duniya cewa, Sin da Afrika sun hada hannu don samun nasara tare.
Sai dai duk da irin wannann ci gaba da sasan biyu suka, kasashen yamma, sun sha yiwa wannan alaka wata mummunan mahuguwar fahimta, har ma suka neman bata wannan dangantaka ta fannoni daban-daban. Sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe, kuma hakar su ba za ta taba cimma ruwa ba.
Sakamakon wannan hadin gwiwa, kasashen Afrika da Sin, suna kokarin hade manufofi da dabarunsu na samun ci gaba karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da muradun ci gaba masu dorewa na MDD da kuma ajandar raya nahiyar ta kungiyar Tarayyar Afrika da ake son cimmawa nan zuwa shekarar 2063.
Misalin abubuwa na baya-bayan nan da wasu kasashen Afirka suka amfana da shi daga alakarsu da kasar Sin sune, filayen wasan da suka hada da na Korhogo da na San Pedro, baya ga filin wasa na Alassane Ouattara da aka kaddamar da gasar wasan cin kofin kwallon kafan nahiyar Afirka na shekarar 2024, a kasar Code D/Ivoire da kamfanin kasar Sin ya gina.
Bayanai na nuna cewa, bisa ga tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kawo yanzu kamfanonin kasar Sin sun gina layukan dogo a Afirka da tsawonsu ya zarce kilomita dubu 10, baya ga hanyoyin mota da suka kai kusan kilomita dubu 100, da gadoji kusan dubu da tashoshin jiragen ruwa kusan dari, da ma dimbin asibitoci da makarantu da filayen wasa.
Masana na ganin cewa, irin wadannan ayyuka za su inganta da ma saukaka harkokin zirga-zirga, baya ga kara samar da kudaden shiga, matakin da zai kara inganta rayuwar mazauna wuraren. Wannan na kara tabbatar da cewa, kasashen Sin da Afirka na kara zama tsintsiya madaurinki daya.