Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbaci, musamman al’ummar musulmai, cewa ba wani maniyyancin Nijeriya da zai rasa aikin hajji 2025, kuma za a gudanar da aikin hajji cikin sauki, lafiya da nasara.
Ya umarci hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) da ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen tabbatar da an yi aikin hajjin cikin lafiya ba tare da wata matsala ba, kuma kowani maniyyanci ya samu damar sauke farali.
- Nijeriya Na Iya Fuskantar Ƙarancin Maniyyata A Hajjin Bana
- NAHCON Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2025 zuwa 10 ga Fabrairu
Wannan umarnin na zuwa ne bayan da mataimakin shugaban kasan ya gana da shugabannin hukumar NAHCON a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Litinin.
Shettima ya kira zaman ne bayan rahotannin da ke cewa takaddamar kwantiragi a tsakanin masu hidima na Saudiyya, Masharik Al-Dhahabiah, zai janyo rashin samun biza ga maniyyatan Nijeriya.
“Ba za mu taba bari wani maniyyancin Nijeriya ya rasa aikin hajjin 2025. Tabbas babu makawa aikin hajji zai wakana, sannan kowani irin kalubale da za a fuskanta za a shawo kansa a kan lokaci,” Shattima ya tabbatar.
Mataimakin shugaban ya umarci shugabannin NAHCON da su gaggauta daukan kwararan matakan da suka dace domin tabbatar da kare martabar dukkanin maniyyatan Nijeriya.
Da yake magana kan soke kwantiragin da suka yi da kamfanin kasar Saudiyyan, shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Saleh Usman, ya ba da tabbacin cewa lamarin ba sai shafi kowani maniyyancin Nijeriya ba.
“Ba wani abun damuwa kwata-kwata. Ba wani maniyyancin Nijeriya muddin an masa rajista da za a bar shi,” Usman ya shelanta.
Ya kuma yi watsi da zargin da kungiyar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi (FSPWA) ke yi na cewa takaddamar kwangilar na iya kawo cikas ga aikin hajjin.