A farkon makon nan ne haɗaɗɗiyar Ƙungiyar matasan Arewa, wacce ta haɗa ƙungiyoyi 16 daga sassan jihohin Arewacin ƙasar nan suka gudanar da wani taron manema labarai a Kaduna domin nuna rashin amincewarsu da shirin gwamnatin Tarayya na mayar da wasu muhimman sassan babban bankin Nijeriya, CBN daga Abuja zuwa Legas.
Taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na Arewa House, Shugaban tawagar ƙungiyoyin, Malam Murtala Abubakar ne ya jagoranci zaman, inda ya bayyana cewa “A yau mun haɗa ku a nan ne domin mu nuna adawarmu da damuwarmu kan shawarar mayar da wasu muhimman sassa guda biyar na Babban Bankin Nijeriya (CBN) daga Abuja zuwa Legas.
- Ana Tuhumar Sojoji 30 Kan Yunkurin Juyin Mulki A Saliyo
- Sudan: Aiwatar Da “Yarjejeniyar Jiddah” Za Ta Shimfida Zaman Lafiya – Gwamnati
“Da kuma batun mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayya (FAAN) da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya ta yi daga Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya zuwa Legas.”
Murtala ya kara da cewa, “Mu, ƙungiyoyin matasan Arewacin Nijeriya, muna wakiltar murya da muradun miliyoyin matasa daga yankin Arewacin ƙasar nan, waɗanda wannan shawarar ta shafa. Mun yi imanin cewa ba kawai ayyukan rashin gaskiya ba ne, har ma da illa ga ci gaban tattalin arziki, zamantakewa da siyasa na yankin Arewa da ma ƙasar baki ɗaya.”
Da ya ke tsokaci game da sassan masu muhimmanci da Babban bankin zai ɗauke zuwa Legas, Malam Murtala cewa ya yi, “Muna tambayar dalilan da ya sa Babban Bankin ƙasa ɗaukar wannan mataki a kan muhimman sassanta biyar, waɗanda suka hada da sashen Kula da Harkokin Bankuna; Sashen Kula da Sauran Cibiyoyin Hada-hadar Kuɗi; Sashen Kula da Buƙatun Masu hulɗa da Bankuna; Sashen Tsarin Sarrafa Biyan Kuɗaɗe da Sashen Dokokin Hada-hadar Kuɗi.”
Babban Bankin ya kawo hujjar ɗaukar wannan mataki komawa Legas, inda ya ce ya ɗauki wannan tsari ne domin rage cunkoso a babban ofishinsa da ke Abuja, wanda aka gina domin ma’aikata 3,000, amma yanzu yana da 4,000.
To, amma sai dai Matasan sun yi nuni da cewa, wannan dalili ba shi da ƙarfi, domin babban bankin zai iya faɗaɗa ofishin nasa a Abuja cikin sauƙi, ko kuma ya raba
ma’aikatan nasa zuwa wasu yankuna, maimakon ya tattara su a Legas.
Ƙorafi da koken matasan Arewar, ba a kan Babban Bankin kaɗai ya tsaya ba, sun kuma yi tir ga Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya bisa matakin da ta ɗauka na mayar da hedikwatar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAAN) zuwa Legas, “Wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idar ɗa’a ta tarayya da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya,” in ji matasan.
A ƙarshe, matasan sun jawo hankalin gwamnati da cewa, “Muna kira ga Gwamnatin tarayya ta janye waɗannan matakan da Babban Bankin ƙasa da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama suka ɗauka cikin gaggawa, sannan ta dawo da martabar Abuja, Babban Birnin Tarayya.
An zabi Abuja ne a matsayin babban birnin ƙasar nan don zamowarta a tsaka-tsaki ga jinsunan da yankunan kasar. Har ila yau, Abuja tana taimaka wa wajen daidaitawa ga yankuna da sassa daban-daban na kasar nan.
Ƙungiyoyin da suka haɗu a wannan taro, sun haɗa da ‘Arewa Defense League, Association of Northern Nigerian Students, Arewa Youth for Development and National Unity, Arewa Young Women’s Rights Advocate Council, Northern Youth in Defense of Democracy, Arewa Radio and Television Commentators, Northern Youth Democratic Agenda Da kuma The Time is Now, the Time is Ours Association.’
Sauran sun haɗa da ‘Arewa Youth Advocate for Peace and Unity Initiative, Northeast Youth Artisans Association, Bauchi State Citizens Action for Chang, Youth Initiative for Good Governance, Coalition of Tiv Youth Organization, Matasan Arewa Ina Mafita Development Association, Toro Youth Circle da Northern Youth Coalition Forum.