• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Za Mu Bari NNPP Ta Yi Magudin Zabe A Kano Ba —Gwamnatin Kano

by Sadiq
3 years ago
Zabe

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jam’iyyar APC ta sha alwashin tabbatar da hana duk wani yunkuri da ‘yan adawa za su yi na yin magudi a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a gudanar a jihar a ranar 11 ga watan Maris.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba, ya fitar ranar Litinin a Kano.

  • An Fara Bincike Kan Sojan Da Ya Kashe Abokin Aikinsa, Ya Kuma Hallaka Kansa A Sakkwato 
  • Kotun Koli Ta Tabbatar Lawal Dare A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Zamfara 

Ya ce dole ne gwamnati ta jawo hankalin jama’a “saboda hakan na iya kawo cikas ga zaben gwamna da na ‘yan majalisun da za a yi.

Ya kuma kara da cewa gwamnati ta samu sahihin bayanai kan yadda za a dauki ‘yan baranda daga kauyukan Kano da wajenta domin tada zaune tsaye a zaben ta hanyar tashin hankali, magudin zabe, kwace akwatuna da kone-kone.

Garba ya kara da cewa, a shekarar 2019 ‘yan adawa sun gudanar da wani shiri na magudin zabe, musamman a kananan hukumomi, inda matasa, wadanda galibi ba su da katin zabe, suka daura damarar yin aika-aika.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

Kwamishinan ya yi zargin cewa a wannan karon ‘yan adawa na shirin kawo hargitsi ta hanyar amfani da ‘yan baranda don tayar da tarzoma da nufin tarwatsa masu kada kuri’a a rumfunan zabe domin samun damar yin magudin zabe da kuma karkatar da ra’ayin jama’a.

Ya kuma yi zargin cewa sanarwar da ‘yan adawa a jihar suka fitar wasa ne kawai amma sun kammala munanan shirye-shiryensu na ganin sun kawo cikas a harkar zabe tare da tayar da tarzoma.

Sai dai Garba ya ba da tabbacin cewa gwamnatin APC za ta tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a jihar.

Kwamishinan ya yi kira ga jami’an tsaro da abin ya shafa da su kasance cikin shiri don sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar kama duk wani mutum ko wata kungiya da ke da niyyar tayar da fitina don hana mutane yin amfani da ikonsu.

Leadership Hausa ya rawaito cewa babbar jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar, a ranar Litinin ta sanar da mazauna jihar ta hanyar wani taron manema labarai kan shirin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi na murza tsarin dimokuradiyya ta hanyar tsoratar da masu zabe.

Don haka jam’iyyar New NNPP ta bukaci hukumomin tsaro da su samar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tashin hankali ba.

Wani jigo a jam’iyyar, Dokta Bappa Bichi, ya shaida wa manema labarai cewa, muradin ‘yan Nijeriya na zaben shugabannin da suke so ba zai yiwu ba idan hukumomin tsaro suka kasa samar da daidaito ga dukkanin jam’iyyun siyasa.

A cewarsa, hakan zai ba da damar gudanar da zabe na gaskiya da adalci.

Bichi ya kuma bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da hukumomin tsaro da su kasance a tsaka-tsaki da adalci da kuma rashin nuna banbanci wajen gudanar da ayyukansu a lokutan zabe da kuma bayan zabe.

A baya dai rundunar ‘yansandan jihar ta gargadi jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu da magoya bayansu kan duk wani tashin hankali.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya kuma bayar da tabbacin ba za su dauki bangare a zaben ba.

A cewarsa, hukumomin tsaro sun kuduri aniyar tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da kama tare da hukunta wadanda suka tada tarzoma kamar yadda aka yi a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
Labarai

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Labarai

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
tinubu
Labarai

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Next Post
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe

Ka Daina Gararamba A Titi Ka Tafi Kotu —Martanin APC Ga Atiku

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025
tinubu

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

November 4, 2025
2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

November 4, 2025
Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

November 4, 2025
Karancin Abinci: Kofar Ofishin Tinubu A Rufe Take, Har Wasu Ministoci Ba Su Iya Ganinsa – Ndume 

Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume

November 4, 2025
Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.