Ba Za Mu Yi Wasa Da Damar Da Muka Samu Ba – Guardiola

Daga Abba Ibrahim Wada

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa ba za suyi wasa da damar da suka samu bat a zuwa wasan karshe na kofin zakarun turai na wannan kakar.

Guardiola wanda ya bayyana farin cikinsa da yadda Manchester City ta samu zuwa wasan karshe na gasar zakarun Turai a karon farko bayan lallasa kungiyar kwon kafa ta PSG kuma yanzu yana fata tawagarsa ta samu sa’a a wasan karshen.

Manchester City, wadda itace Jagorar gasar Firimiyar Ingila ta samu nasarar doke kungiyar PSG da ci 2-0 a filin wasanta na Etihad a wasa na biyu na wasan kusa da karshe na gasar zakarun nahiyar Turai, bayan nasara 2-1 da ta yi a Parc des Princes.

dan wasan Algeria, Riyad Mahrez ne ya ci dukkanin kwallayen da Manchester City ta ci a daren ranar Talatar, inda aka tashi wasa 4-1 a jimilce a kan PSG kuma ta karasa wasan ne da mutane 10 bayan jan kati da aka bai wa dan wasanta Angel Di Maria.

Manchester City wadda bata taba buga wasan karshe ba zata kece raini da kungiyar kwallon kafa ra Chelsea wadda ta karbi bakuncin Real Madrid a filin wasa na Stamford Bridge a ranar Larabar data gabata.

A wasan farko dai kungiyoyin Chelsea da Real Madrid Kunnen doki 1-1 suka buga sannan a wasa na biyu da aka fafata a filin wasa na Stamford Bridge Chelsea ta samu nasara daci 2-0 ta hannun ‘yan wasanta Timo Werner da Marson Mount.

Exit mobile version