A ranar Lahadi kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya jagoranci wasansa na ƙarshe a matsayin kocin ƙungiyar bayan shafe shekaru 9 a Anfield.
Klopp wanda tsohon kocin Borrusia Dortmund ne ya lashe kofuna 8 a Liverpool da suka haɗa da; Gasar Zakarun Turai da Firimiya da UEFA Super Cup a shekarun da ya kwashe a ƙungiyar.

A wasansa na ƙarshe a ranar Lahadi Liverpool ta doke ƙungiyar Wolverhampton Wanderers da ci 2-0 a filin wasa na Anfield.
Bayan an tashi daga wasan magoya bayan Liverpool sun yiwa kocin nasu bankwana mai ƙayatarwa yayinda ya tabbatar da cewar ba zai taba mantawa da ƙungiyar a rayuwarsa ba.