Shafin RUMBUN NISHADI shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jaruman finafinan hausa daga cikin masana’antar Kannywood, har ma da kanana. Inda a yau shafin yayi cozali da daya daga cikin jaruman da suke taka rawa a yanzu wato, AISHA UMAR wacce aka fi sani da AISHA KAMSHI, ya yin da ta bayyanawa masu karatu wasu batutuwa da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta ta fim.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.
Aisha Umar, amma an fi sanina da Aisha Kamshi.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni a a ‘Delta state’, na yi makarantar firamare da sakandare a Delta, sannan nayi aure a can. Yara na uku, Allah ya kawo rabuwa tsakani na da mijina. Babana dan ‘Nasarawa State’ ne, Mama ta kuma ‘yar Jihar Kano ce. Shekaruna Talatin da hudu, na tsinci kaina a masana’antar Kannywood ne shekara shida da suka wuce baya.
- Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad
- Babu Wanda Ya Jawo Ra’ayina Zuwa Masana’antar Kannywood —Umar Hassan (2)
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Saboda fim yana daya daga cikin abin da ya fara burge ni bayan aure na ya mutu, shi fim abu ne wanda yake kamar wa’azantarwa da kuma tunatarwa.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Yadda gwagwarmayar ya kasace shi ne; na zo fim ne ba tare da tunanin yadda za ta kasance da ni ba, amma yanzu kam Alhamdulillah.
Ya batun iyaye lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su?
Eh, a gaskiya na samu. Saboda mahaifiya ta da ‘yan’uwana sun ki yarda, sai da na samu na zaunar da su na fahimtar da su sannan.

Da wane fim ki ka fara?
‘Motsin Rai’ wanda Yahaya Sa’id ne yayi daraktin, da kuma Dadin Kowa.
Ya farkon farawar ta kasance?
Gaskiya na sha wahala kasancewar shi ne farkon dasa min ‘camera’.
Da su wa ki ka fara cin karo a farkon shigarki kannywood?
Bosho, su Dan’Auta da sauransu.
Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
Gaskiya ba zan iya kirgawa ba.
Cikin finafinan da ki ka fito wanne ne ya zamo bakandamiyyarki?
Kishiyar uwa, saboda na fito a mahaukaciya abun dai abun armashi.
Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?
Dalilin fim na je gurare wanda ban da ta wannan hanya, ban yi tunanin zuwa ba.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta cikin masana’antar?
Eh, kam ba za a rasa ba, to, amma Alhamdulillah.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka, wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwa?
Kamar mutuwar mahaifi na, ba zan taba iya mantawa ba har abada.
Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?
Eh, ina da shi.
Kafin shigarki masana’antar Kannywood wadanne jarumai ne suke burge ki, kuma me ya sa?
Ali nuhu, saboda yadda yake aikinsa kamar a gaske.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
In zama babbar jaruma.
Bayan fim kina wata sana’ar ne?
Eh, ina ‘business’.
Misali wani daga cikin abokan aikinki ya ce yana sonki zai aure ki, shin za ki amince ki aure shi ko kuwa ba ki da ra’ayin auren dan fim?
Idan da so da kauna me zai hana.
Wasu na kokawa game da masana’antar kannywood, a takaice ya za ki yi wa masu karatu bayanin yadda masana’antar take, shin wace ce Kannywood ya cikinta yake?
Kannywood wata masana’anta ce wacce take kamar makaranta, kafin ka fara ta, dole sai ka mayar da hankali.
Wane kira za ki yi ga masu kokarin shiga kannywood?
Duk wacce za ta shigo ta dauka kamar koyan sana’a ce ya kawo ta, dole sai ta mayar da hankali tare da jajircewa.
Ko akwai wata shawara ko wani sako da ki ke da shi ga sauran abokan aikinki?
Sako na a gare su shi ne, su dinga rike gaskiya da amana, su sani mu kamar amana muke a hannunsu, su taya mu rike ta kima da mutuncin mu.
Me za ki ce da masoyanki masu kallon finafinanki?
Ina yi wa kowa fatan alkairi.
Muna godiya
Ni ma na gode.














