Babban Kantin ShopRite Zai Fice Daga Nijeriya

Babban kantin nan na Shoprite ya ce yana duba yiwuwar daina gudanar da harkokin kasuwancinsa a Nijeriya. A wata sanarwa da ya fitar yau litinin da safe, masu kantin sun dauki matakin janyewa daga Nijeriya ne saboda an samu mutanen da suka nuna sha’awar sayen hannun jarin kamfanin.

Babban kantin ya ce annobar korona ta yi tasiri sosai a kan harkokin kasuwancinsa a kasashe 14 na Afirka inda aka samu raguwar sayen kayansa da kashi 1.4, ko da yake a Afirka ta Kudu an samu ba haka batun yake ba.

Mr. Ini Achibong, ya shaida wa manema labarai, cewa masu kantin sun dade suna neman mutanen da za su saye shi, amma babu abin da zai sauya game da yadda yake gudanar da harkokinsa a kasar a wannan lokaci.

Shoprite ya bude kanti a Nijeriya ne tun a shekarar 2005, wanda ya bayyana a matsayin inda yake “sayar da dukkan, ko akasarin kayansa.”

A shekarar da ta wuce, matasa sun kai harin ramuwar gayya kan wasu kantunan na Shoprite da ke Najeriya sakamakon zargin musgunawa wasu ‘yan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu. Matasa da dama kan yi wa kantin Shoprite tsinke a lokutan bukukuwa inda suke yin sayayya sannan su dauki hotuna.

Exit mobile version