A kwanaki ne aka kaddamar da babban masallacin Juma’a na unguwar Adogba da ke garin Ibadan wanda Mai Alfarma Sultan na Sakkwato Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya jagorancin budewa, Gwamnan Jihar Oyo ‘Seyi Makinde ya gina, bayan da aka rusa tsohuwar masallacin a shekarar 2019 don sabunta ta don samar da karin fahimtar juna da kuma kawar da bambancin kabilanci da na addini.
A lokacin da gwmanatin jihar Oyo ta rusa masallacin Adogba wanda ake kuma kira da ‘Organisation of Tadhamunul Muslimeen Moskue’, da ke Adogba, a kan hanyar Iwo a cikin garin Ibadan a shekarar 2019 don samar da babbar tashar mota ta ‘Iwo Road’, da yawan al’umma ba su natsu da yadda aka rusa masallacin ba, amma tabbacin da gwamnan Jihar Oyo, ‘Seyi Makinde ya bayar na cewa, za a gina sabon masallaci ya sa al’umma Musulmi duniya suka natsu tare da jin dadin lamarin.
- Zargin Baɗala: Hisba Ta Kama Mata Da Maza A Zamfara
- Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Wucin Gadi Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila
Shekara 4 bayan rusau da aka yi a daidai ranar 16 ga watan Nuwamba 2023 Makinde ya cika alkawarin da ya yi na sake gina babban masallacin Adogba daga cikin kudi mallakin kansa, a inda shugaban majalisar koli ta addnin musulunci kuma Sultan na Sakkwato, Mai Martaba Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, tare da rakiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da Gwamna ‘Seyi Makinde suka jagoranci kaddamarwa.
Kasancewar Shugaban Al’umma Musulmun Nijeriya, Sultan Abubakar da mai martaba Sarkin Kano da kuma wasu manyan jagororin Musulmi a Nijeriya ya kara bayyana bukatar karfafa fahimtar juna a bangaren addini da kabilanci, duk kuwa da matsalolin da Nijeriya ke fuskanta.
A jawabinsa, Gwamna Makinde ya yaba wa al’ummar Musulmin Jihar Oyo a kan goyon bayan da suka bashi a zaben gwamnan da aka gudanar ranar 8 ga watan Maris 2023, ya kuma kara jaddada kudirinsa na gudanar da mulkin jihar tare da yin adalci da dukkan ma’abuta addinan da ke jihar.
Makinde ya kuma bayyana cewa, a lokacn da aka yanke shawarar rusa babban masallacin Adogba da wani coci da suke a kan inda gwamnantin jihar ta ke son gina babban tashar mota, an samu rashin jituwa daga bangaren al’umma muslmi, “Domin kuwa wasu na ganin lamarin a mastayin kamar an nuna banbanci”.
Ya kuma ce, “Na je na yi sallah tare da al’umma a masallacin, na yi musu bayanin cewa, masallacin tare da wani coci ne za a rusa saboda mun riga mun shirya gudanar da aikin babbar tashar mota, saboda muhimmancinta ga al’ummar jihar.
“Na fahimamci akwai rashin fahimma a tsakanin al’umma da gwamnati don ko kafin in kammala jawabi na har wasu sun fara gunaguni.
“Amma bayan da na yi jawabi a masallacin a ranar, sai na ga kusan kashi 90 na mutanen sun yarda da magana na, a kan haka kusan duk lokacin da na rasa kudin aikin masallacin (saboda na gina masallacin ne da kudin kashin kaina) sai in tuna kashi 90 na mutanen da suka yi Imani da abin da na fada musu, na cewa zan sake gida musu masallacin kamar yadda na yi alkawari, wannan yake karfafa ni”.
A nasa jawabin, mai martaba sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Addnin Musulunci, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yaba wa Gwamna a kan yadda ya yi alkawarin gina masallaci ya kuma cika alkawarin.
Ya kara da cewa, “Idan ka kalli yadda masallacin yake a da da kuma yadda ya zama a halin yanzu ba abin da zaka ce sai mika godiya ga Allah a kan rayuwar ‘Seyi Makinde a kan tunaninsa da kuma yadda ya aiwatar da tunanin nasa.
“Mutane da dama na furta alkawarin yin wani abu amma in an zo aiwatarwa sai kaga sun samu matsalar cika alkawarin da suka yi,” in ji shi.
Sultan ya kuma lakaba wa gwamnan na jihar Oyo sunansa na ‘Sa’ad’ a kan yadda ya yi alkawari na gina dakin Allah ya kuma cika alkawarin, ya ce, sabon masallacin wanda ke da makarantar Islamiya zai taimaka wa al’umma wajen samun ilimi duniya da na gobe kiyama.
Sultan ya kuma kara jaddada cewa, “Ana kira na Sa’ad, amma a yau zan sanya maka suna Sa’ad. Muna godiya ga Allah da ya kawo mu garin Ibadan muka halarci wannan al’amari mai matukar muhimmanci.
“Kusan shekara uku da suka wuce na yi magana da gwamnan, ya gaya mani cewa yana gina masallaci a wani wuri mai muhimmanci a garin Ibadan, na ce masa na san wurin, ya kuma ce, ni zan kaddamar da masallacin in an gama na kuma amsa masa cewa, lallai zan zo don kaddamarwar da yardar Allah.
“Na zagaya yankin gaba daya, ina mai tabbatar muku da cewa, babu wani gini da ya kai wannan masallacin kyau. Duk ta inda ka fito zaka ga masallacin abin da ya kamata mu rinka yi kenan ga al’ummarmu. Ya kamata mu rika gina dakunan Allah masu kyau.
“Masallaci ba wai wurin bauta kadai ba ne, ya kuma kasance makaranta. A yanzu mun samu makarantar Islamiyya da kyakyawar masallaci, abu ne da zai karfafa mana neman ilimin duniya da na lahira. Saboda haka ya kamata mu yi amfani da makarantar wajen ilimantar da kanmu, ‘yanuwanmu da sauran al’umma don mu zauna lafiya da juna ba tare da wata matsala ba.
“Wannan tarihi ne mai kyau muna fatan a samu irinsa a wurare da dama, saboda haka muna godiya ga mai girma Gwamna,” in ji Sultan Abubakar.
Daga karshe ya kuma nemi a tabbatar da kula da masallacin yadda ya kamata.
A nasu martanin, wasu al’umma Musulmi sun yaba wa Gwamnan Jihar Oyo, ‘Seyi Makinde, sun kwatanta shi da mai cika alkawari, sun ce basu taba tunanin zai cika allawarin da ya yi a shekarar 2019 na gina masallacin ba.
Wani mai sallah a masallacin, mai suna Mista Olawole Abdulfatah, ya ce, bai taba tunanin gwamnan zai cika alkawarin da ya yi ba, don ya yi tunanin alkawari ne irin na ‘yan siyasa da basa cikawa.
Shi kuwa wani mai suna Mista Ganiyu Adebayo, ya ce, kasancewar Saltan da sauran manyan manyan al’umma musulmi daga arewacin kasar nan wata manuniya ce na cewa, ana mutunta Gwamna Makinde a sassan Nijeriya saboda karfafa fatimtar juna a tsakanin kabilu da addinai a Nijeriya.
Wasu da suka yi jawabi a wajen taron sun bayyana cewa, hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma yana da matukar muhimmanci ga ci gaban Nijeriya. Sun kuma yaba wa Gwamna Makinde a bisa hangen nesansa na karfafa hadin kai da zaman lafiya ba wai na Jihar Oyo ba harma da Nijeriya baki daya.
Wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayyar Nijeriya, Alhaji Yayale Ahmed, manyan malaman addinin musulunci da manyan ma’aikatan gwamnati.