Babbar Kotu Ta Tabbatar Hukuncin Rataya Kan Matashin Da Ya Kashe Budurwarsa A Yobe

Babbar kotun (State High Court) da ke jihar Yobe ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga matashi Muhammed Adamu, wanda ta samu da laifin halaka budurwarsa a kwanan baya, mai suna Hauwa Muhammad.

Da ya ke zartar da hukuncin, Mai Shari’a A. Jauro, ya bayyana yadda kotun ta samu wanda a ke zargin da laifin kisa a karkashin ayar doka, ta sashe na 221 ta ‘Penal Code’.

Mai Shari’a Jauro ya kara da cewa, kotun ta samu kwararan hujjoji bisa yadda wanda a ke zargin ya halaka Hauwa bisa ga rajin kansa.

Hukuncin ya nuna cewa: “Bisa la’akari da ayar dokar manyan laifuka ta sashe na 273 (Criminal Procedural Code), ta bayyana cewa idan an yanke wa wani mutum hukuncin kisa, to za a rataye wuyanshi har sai numfashinsa ya dauke.

“Saboda haka, a matsayina na Mai Shari’a, na yanke maka hukuncin  kisa, Muhammed Adamu ta hanyar rataya. Ina rokon Allah ya gafarta maka,” in ji Mai Shari’a Jauro.

A jawabin lauya mai kare wanda ake kara, Barista M. Dauda, ya bayyana cewa zai dubi hukuncin a tsanake tare da nazarin yiwuwar daukaka kara.

A hannu guda kuma, a zantawar wanda aka zartaswa da hukuncin kisan ga manema labarai, ya ce, “Tun farko addu’a ta ga Allah ita ce in samu ayi min hukuncin da ya dace.

“Kuma na yi imani kan cewa abinda Allah ya zaba zuwa gare ni kenan kuma hakan shi ne zabin Allah,  Santana kuma na karba da hannu  biyu.”

Idan dai za a iya tuna wa, ranar biyar b (5) ga watan Yunin 2018, rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama Adamu da zargin kashe budurwar sa Hauwa, a cikin watan Mayun 2018.

Exit mobile version