Zubairu M Lawal
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya yi kira ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC mai mulki da su yi amfani da lokacin gabanin zaben 2023, don kawar da matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar APC.
Gwamnan ya ce a yi kokari a hada kai a samu sulhu da kuma kwantar da hankulan ‘ya’yan jam’iyyar, musamman abin da ya faru bayan zaben fid da gwani.
Injiniya Sule ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakoncin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, yayin da ya kai ziyarar gaisuwar Sallah da ta’aziyya a fadar gwamnatin da ke Lafiya a ranar Asabar.
A cewar gwamnan, ya zama wajibi jam’iyyar APC ta shiga zaben 2023 a dunkule cikin hadin kan ‘ya’yanta tare da zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga shugaban jam’iyyar APC na kasa da ya yi amfani da kwarewarsa wajen kawar da tashin hankalin da ke kara ta’azzara a cikin jam’iyyar.
Ya ce, saboda abubuwan da suka faru a sakamakon zaben fid da gwani na jam’iyyar APC da aka kammala kwanan nan, lamarin da ya sanya wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka rika ficewa daga APC zuwa wasu jam’iyyun. Ya ce, da dama membobin jam’iyyar APC masu rike da mukamai sun fice daga jam’iyyar saboda da zargin rashin adalci da aka yi masu a lokacin zaben. Gwamnan ya ce lamarin ya shafi ko’ina cikin fadin kasar nan.
“Kusan watanni takwas kafin zabe, wannan ya rage gare mu musamman tsofaffin ‘yan siyasa irin ku, mu yi amfani da damarmu wajen kwantar da hankula da duk wadanda suka ji rauni. Mu kuma janyosu su dawo cikinmu hakan shi ne damarmu na samun nasara.
” Ya zama wajibi mu yi duk mai yuhuwa wajen ganawa da sauran ‘ya’yan jam’iyyar domin sulhuntawa”.
Hakazalika, gwamnan ya yi kira ga masu taimaka wa shugaban jam’iyyar na kasa, su ma su yi amfani da wannan damar wajen tuntubar ‘ya’yan jam’iyyar dan jin ra’ayinsu da kuma kauce wa al’amuran da ka iya haifar da matsala ga jam’iyyar nan gaba.