Biyo bayan tashin gwauron zabi da Tumatari ya yi wanda ya kai sama da kashi 100 a ‘yan watannin da suka gabata, musamman a jihar Legas da sauran wasu jihohin da ke a kasar nan, mai yuwa tashin farashin ya zama barazana na shirye-shiyen da Musulmi ke yi domin gudanar da bukukuwan babbar Sallah da ke tafe, duba da yadda ake yin amfani dashi wajen dafa difadi-kar Shinkafa.
‘Yan kasuwar da ke yin hada-hadar kasuwancinsa, sun dangan-ta wannan tashin farashin kan sauyawar kakar nomansa.
Kazalika, sun yi ikirarin cewa, isowar Tumatir din da aka noma a cikin rani a sassan kasar nan, inda wanda aka noma a yanzu lokocin girbinsa an rigu da yawan wanda ake kai wa kasuwa domin sayar wa.
- Yawan Wutar Lantarki Da Jerin Madatsun Ruwa Dake Sin Suka Samar A Rubu’in Farko Na Bana Ya Zarce Kilowatts Biliyan 52
- Alkiblar Da Nijeriya Ta Dosa Cikin Shekara 25 Na Dimokuradiyyarta
Malam Umar Tanko wani mai sayar da Tumatir a kasuwar Mile 12 a jihar Legas ya sanar da cewa, Kwando daya na danyen Tu-matir mai kyau, a watan Afrilun da ya wuce, an sayar dashi daga Naira 50,000 zuwa Naira 80,000, amma a yanzu, ana sayar da Kwando daya daga Naira 140,000 zuwa Naira 150,000.
Ya ce, matsakaicin Kwando daya na Tumatir da bai yi dameji a hanya lokacin da aka yo safarasa daga Arewacin Nijeriya zuwa kudancin kasar nan ba, a yanzu ana sayar dashi daga Naira 60,000 zuwa Naira 100,000, ya danganata da irin damejin da ya yi.
Ya ci gaba da cewa, a watan Afirilun da ya wuce, Kwando daya irin wannan na Tumatir an sayar dashi a kan Naira 30,000.
Kazalika ya bayyana cewa, danyen Tattasai da ake yin amfani dashi a cikin dafadikar Shinkafa, shi ma farashinsa ya tashi wanda farashin har ya rubanya na watan da gabata.
Umar ya kara da cewa, a watan da ya wuce, farashin Bokiti daya na danyen Tattasai, an sayar dashi daga Naira 3,000 zuwa Naira 4,000, amma a yanzu ana sayar dashi kan Naira 8,000.
Shi ma wani mai sayar da Tumatir a kasuwar Ikorodu da ke a ji-har Legas Shefiu ya danganta tashin farashin na Tumatir saboda rage kawo shi ganin cewa, kakar rani ta nomansa, ta wuce.
A cewarsa, “ A watan da ya wuce, mun sayar da Bokiti daya kan daga Naira 4,000 zuwa Naira 5,000, amma a yanzu, muna sayar da Bokiti daya kan Naira 10,000, nawa ma akwai sauki domin na sayo shi ne daga Kano ba daga kasuwar Mile 12”.
Lamarin na hauhawan farashin ya kuma karade sauran wasu jihohin kasar nan kamar a Edo, Abuja, da Delta da sauransu.
An ruwaito cewa, wasu mazauna wadannan jihohin ba sa ma iya sayen kwayar Tumatir daya a kan Naira 500 duba da yadda ake sayar da Kwandon sa daya daga Naira 120,000 zuwa Naira 140,000.
A garin Onitsha na jihar Anambra, farashin Kwando daya na danyen Tumatir ya kai daga Naira 110,000 zuwa Naira 140,000.
Bugu da kari, a watan Afirilun da ya wuce, Hukumar Kiddiga ta Kasa wato (NBS) a cikin rahoton da ta fitar na hasashen tashin farashin kayan abinci ta bayyana cewa, farashin kilo daya na Tumatir ta karu da kashi 131.58 a cikin dari a 2023 da kuma a cikin watan Afirilun 2024.
Sai dai, rahoton hukumar ya bayyana cewa, a tsakanin watan Maris da watan Afirilun 2024, farashin kilo daya na Tumatir, ya karu zuwa kashi 17.06 a cikin dari.
Kazalika, a cikin wani rahoton hasashe da SBM ta fitar ya bay-yana cewa, a watan Maris din 2024, dafa Shinkar dafadika ta hanyar yin amfani da Tukunyar Isar Gas a mayan biranen da ke a kasar nan, farashin ya karu zuwa Naira 17,000 2024, sabainin yadda ya kai na Naira 13,106 watan Okutobar 2023.