A duk lokacin da aka bullo da wata manufa ko hadin gwiwa da nufin inganta rayuwar al’ummomin kasashen duniya, ya kamata kowa ya ga sakamakon hakan a zahiri, kamar yadda shawarar “ziri daya da hanya daya” ta samarwa kasashen da ke cikinta da ma hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka da ya haifar da gagarumin sakamakon, sabanin yadda Amurka da kawayenta ke neman bata sunan shawarar yayin taron G7 na baya-bayan da suka gudanar a kasar Jamus.
Sai dai duk wani surutu da Amurka da masu neman bata sunan shawarar za su yi, hakarsu ba za ta cimma ruwa ba, domin kan Mage ya riga ya waye, galibin kasashen da suka amfana da shawarar, ba za su taba yarda a yi musu sakiyar da babu ruwa ba.
Har kullum kasar Sin wadda ta gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, tana maraba da duk wata shawarar da za ta inganta muhimman ababen more rayuwar al’ummar duniya. A hannu guda kuma, tana nuna adawa ga duk wani yunkuri na bata sunan shawarar “ziri daya da hanya daya”, bisa hujjar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, don cimma wani muradun siyasa.
Wannan batu na zuwa ne, yayin da shugaban Amurka Joe Bide a wajen taron kolin kasashen G7, ya sanar da kaddamar da wai, wani shirin hadin gwiwa kan inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma da zuba jari a duniya”, har ma wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka da ba’a san ko su waye ba, sun rika furta kalamai na shafawa shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kasar Sin bakin fenti. Duniya ta sha jin surutu da alkawura daga bangaren Amurka ba tare da cikawa ba.
Wani abin takaici ma shi ne, wai kasar da ba ta wadatu da ababen more rayuwa a cikin gidan ta ba , ita ce za ta jagoranci aiwatar da abin da ake kira ayyukan samar da ababen more rayuwa a duniya. Amma idan mutum ya ce, zai ba ka riga to ka kalli ta wuyansa.
Idan ba a manta ba, a yayin taron G7 da aka gudanar a shekarar da ta gabata, an bijiro da maganar shawarar hadin gwiwa da ake kira “Sake gina duniya mai kyau” (B3W), tare da shirin zuba jarin sama da dalar Amurka tiriliyan 40 kan bukatun kayayyakin more rayuwa a kasashe masu tasowa. A wancan lokacin, Biden ya ce shirin zai fi dacewa da bukatun samar da ababen more rayuwa na kasashe daban-daban fiye da shirin “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar.
Amma rashin tsari da neman cimma moriya ta siyasa, wancan shirin bai je ko’ina ba, saboda nuna bangaranci a Amurka. Kuma har zuwa wannan lokaci adadin kudaden da aka saka a cikin ayyukan da ke da alaka, dalar Amurka miliyan 6 ne kawai, karya fure take ba ’ya’ya”.
Sanin kowane cewa, kasashe masu tasowa suna fuskantar babban gibin kudade wajen gina ababen more rayuwa. Idan har da gaske ‘yan siyasar Amurka suna son ba da taimakon kudi, wannan abu ne mai kyau.
Amma idan har ba sa son baiwa kasashe masu tasowa gudummawa, sai neman su yi wasa da hankali ne, to duk wasu sabbin sharuddan da suka kirkira, ba za su iya yaudarar kasashen da suka amfana da fa’idar shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar ba. Ruwan da ya duka ka, shi ne ruwa.