Tsohon Gwaman Jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya shelanta cewa babu wani aibu idan aka zabi shugaba da mataimakinsa Musulmai a matsayin wadanda za su shugabancin kasar nan a kakar zaben 2023.
Ya sanar da hakan ne a wata hira da manema labarai a gidansa da ke a yankin Bodija da ke a garin Otun a garin of Ibadan.
- NSCDC Ta Bankado Shirin ISWAP Na Kai Hare-Hare A Makarantu Da Cocina A Abuja
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Ta’adda Sun Sako Karin Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
Ladojaya sanar da cewa, akwai bukatar ‘yan Nijeriya su jingine maganar yin amfani da addini a harkar siyasar kasar nan, inda ya yi nuni da cewa, Musulmai da Kiristocin kasar ‘yan uwan juna ne.
Ya ce kamata ya yi ‘yan Nijeriya su mayar da hankali wajen zabar dan takarar da suka san zai iya shugabanci kasar nan, inda ya bayyana cewa, wasu ‘yan siyasar kasar nan na yin amfani da addini ne kawai don su raba kawunan ‘yan kasar.