Yarima Mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya sake jaddada cewa Masarautar Saudiyya ba za ta ƙulla wata dangantakar diflomasiyya da Isra’ila ba har sai an sami ƙasar Palasdin mai ‘yanci tare kasantuwar gabashin Kudus a matsayin babban birninta.
Ya bayyana hakan ne a lokacin ƙaddamar da zaman taro na majalisar Shura, inda ya nuna adawar Saudiyya da matakan Isra’ila kan Palasdinawa, wanda ya bayyana a matsayin karya dokokin kasa da kasa.
- Tsadar Farashi: Yadda ‘Yan Nijeriya Suka Koma Sayen Kaya Masu Araha
- Saudiyya Ta Yi Allah-wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Wa Al’ummar Yobe
Yarima bin Salman ya sake nanata jajircewar Saudiyya wajen goyon bayan samun ƙasar Palasdin mai ‘yanci, tare da nuna himmarsu ga haɗin kai na yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki ɗaya, da neman hanyoyin warware rikice-rikicen siyasa kamar na ƙasar Yemen, da Sudan, da Libiya.
Haka kuma, ya jaddada nasarorin tattalin arzikin Saudiyya, wanda ya haɗa da bunƙasa sassan da ba na mai ba, da raguwar marasa aikin yi, da cigaban da aka samu a fannin yawon buɗe ido, kula da albarkatun ƙasa, da makamashi mai inganci kuma mai ɗorewa.