Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTAUNAWA

Babu Farfesa Ɗan Arewa Mai Shekara 60 Da Aka Haifa A Asibiti —Dakta Jawa

by Tayo Adelaja
October 21, 2017
in TATTAUNAWA
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

DAKTA MUHAMMAD IBRAHIM JAWA, shi ne shugaba wanda kuma ya assasa makarantar koyon haɗa magungunan garagajiyar farko a Nijeriya, bayan wadda ake da ita a Nahiyar Afrika.  Har ila yau sakataren dindindin a matakin aiki na Jihar Yobe, kuma mutum na farko da fara kai wa irin wannan mataki ta fuskar maganin gargajiya a faɗin ƙasar nan. A tattaunawarsa da wakilinmu a ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Dakta Jawa ya bayyana sirrin yadda Ƙasashen Chana da Indiya suka kai matsayin da suke kai a yanzu ta fuskar bunƙasar magungunan gargajiya, haka zalika ya bayyana matakan da mai maganin garagajiyar Afirika ya kamata ya taka kafin amsa sunan mai maganin gargajiya. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

An daɗe ana maganar magungunan gargajiya, amma har yanzu ba shi da wani matsayi ta fuskar hukumomin lafiya na ƙasa, ko a ina matsalar ta ke?

Gaskiya akwai matsaloli masu yawa sanin kowo ne bamu daɗe da fitowa daga mulkin mallaka ba, kuma bayan samun ‘yan cin kanmu sai muka shiga cikin wata jarrabawa muka kasa yin la’akari da abubuwan da muke da shi  muka zubar da su muka ɗauki na waɗanda suka mulke mu, kila saboda dalilan siyasa  ko kuma mu kanmu rashin sanin muhimmancin namu al’adun ya sa muka yi watsi da shi, wani lokacin kuma son burgewa ya sa muka bar namu mu ka rungumi kayan aro.

Amma dai dalilan da suka sa hakan suna da yawa, amma dai masana musammana marubuta a duniya masu yawa sun yi duba kuma sun yarda da cewa duk ƙasashen da suka samu kansu cikin irin wannan  fitinar  yawancin waɗanda suka karɓi mulki ne a ire-iren waɗancan ƙasashen masu ƙarancin shekaru ne, kuma ba’a samu waɗanda za su ja kunnensu daga magabatansu ba . Amma dai ala ayyi halin mun samu kanmu da tsarin da muke kai darajar mu, musamman tsarin addininmu, al’adunmu, ilminmu da sana’unmu  sai muka watsar da su.

Ke nan a iya cewa ƙasar Chana maganinsu yayi nisa a duniya, shin wace hanya suka bi har suka kai wannan mataki?

Ƙasar China da kullum ake misali da ita gaskiya na samu damar yin Karatu a can, a binda ya kai ni karatu can batun maganin gargajiya ne, na  koyi abubuwa masu yawa na kuma haɗu da mutane da yawa waɗanda suka san al’adunsu, su kansu akwai zamanin da suka tsinci kansu cikin irin wannan hali suka yi watsi da nasu tsarin, harma an samu wasu daga cikin shugabanninsu da suka ce duk wanda aka samu yana amfani da ilmin kimiyar magnin gargajiya cewa suka yi a yanka su a wannan lokacin.

Amma daga baya da suka ga uwar bari suka fahimci za su shiga cikin fitina, sai suka dawo suka ce ai maganin gargajiyar mu ya zama wajibi mu ci gaba da inganta shi, ko da kuwa bai dace da kimiyar zamani ba, mu ɗauko mu karkaɗe shi mu sa su dace da kimiyar zamani, idan ba mu yi haka ba zamu zama bayi.

Saboda haka gaskiya mun ga tasirin irin wannan shugabancin wanda ya basu damar haɓaka irin nasu tsarin tare da samo masu dalilai na kimiya, kuma Alhamdulillahi sai gashi yanzu kowa ina misali ake da China.

China suna da tarihin maganunuwansu a rubuce tsawon shekara dubu biyar, amma lokacin da suka fahimci kimiyyar kiwon lafiya ta haɓaka sai suka ɗauko wasu sunayen suka yi rubutun da ya dace dana yammacin duniya su ka kai su ka ce na su ne, sai aka kwaɓesu akace ba nasu ba ne wannan, aka ce wannan suna suka sauya, amma ba al’adunsu ba ne.

Sun yi wannan yunƙuri ya kai sau goma, daga nan aka samu shugabanninsu masu hangen nesa suka ce mu koma gida domin abubuwan da muke kai wa ba gaskiya ba ne, idan ka kai abinda ba al’adar ka ba ne duniya ta sani ko an san shi sai an gane ko na ina ne.

saboda haka mu koma ga abubuwan da muka tarar da iyayenmu da a baban bautar mu a kai. Tun zamanin Annabi Nuhu zuwa Annabi Ibrahim, Annabi Musa, Annabi Isa har zuwa Annabi Muhammad SAW duk gyara su ake domin samar da ingantaccen tarihi

Shin maganin gargajiya yana da wani ma’auni ne, kuma meye dangantakarsa da jikin ɗan Adam?

Alhamdulillhai ita duk wata sana’a  da duk wani abu da ake a duniya yana da ƙa’idojinsa, matuƙar ana so a ci nasara sai an cika waɗancan ƙa’idoji, don haka duk abinda aka barshi ba tare da an yi masa ƙa’ida ba to ba za’a samu nasarar da ake buƙata ba.

Maganin Gargajiyar Afirika da muka gada wurin Kakanninmu yana da tsari kamar yadda sauran maganin gargajiya na duniya suke da irin nasu tsarin. Bari ɗauki na farko waɗanda suka ce suna da tarihin shekara ɗari 500 su ne China, sai masu binsu su ne Indiya, su Indiya ma suna cewa nasu ya haura shekara 500, domin shi Buda ya zo Chana kafin ya je Nepal, ya kuma wuce ya tsallaka kogi zuwa Sin watau Chana. Don haka ya ɗauko tsarinsu ma ya auna da na Afirika ya ga ɗaya ne?

Chana a rubutunsu cewa suka yi akwai wani abu guda ɗaya wanda ya ƙunshi zafi da sanyi, idan sanyin shi ya yi ƙasa ko zafin ya yi ƙasa akwai matsala, saboda haka sanyi da zafi ajikin wannan abun dai-dai suke, wannan kuma ya haɗa da jikin mutum da duniya baki ɗaya.

Haka kuma Indiya suka ce a jikin mutum sinadarai ne guda biyu sanyi da zafi, idan sanyi ya rinjayi zafi matsala ce kamar yadda idan zafin ya rinjayi sanyi nan ma matsala ce. Don haka mu ma anan afirika ba mu kauce daga wannan ba ma’auninmu a nan shi ne zafin jika da sanyin jiki.

Bari mu dawo na baturen da ke Magana shi ma an gina shi akan wani sinadarin ɗan ƙarami da ake kira ATOM, kamar yadda aka nuna daga Atom ɗin ne aka samu komai a duniya wanda wani da ake kira John don tom ya ƙirƙira inda ya nuna duk waɗannan abubuwa an fare su ne daga wani abu kamar kwayar Zarra.

Shi kuma ɗaya masanin ya sai ya ce; ya gano cewa wannan Atom ɗin ya ƙunshi wasu abubuwa guda uku baƙi da fari ko da zafi da sanyi saboda duk idan aka ɗauko ma’anarsu za ka tara ma’ana guda ce ko wanne ɗabi’arsa daban, amma suna tarayya a wasu wurare, saboda haka, a wannann lokaci ne aka gane zaman duniya lafiya shi ne zafi da sanyi.

Wannan ya sa idan zafi yayi yawa duniya rikice wa ta ke, haka ma idan sanyi ya tsananta, amma idan zafi da sanyi suka dai-daita sai kaga komai ya dai-daita yadda ake buƙata.

 

Batun makarantar da ka samar domin koyar da maganin gargajiyar, me ka ke son samarwa a wannan farfajiya?

Alhamdulillahi wannan makaranta dalilin kafa ta shi ne, mu dubi ƙa’idojin kiwon lafiya, farko shi ne dole mai magani ya san mutum ya kuma san dai-dai ɗinsa, ya san sassan jikinsa, wanda ya san ba su da lafiya idan ya san wannan sai kuma ya koyi sanin me ne cutar ita kanta, ya ya take, mene sababin cutar daga nan sai ya yi tunanin ya za’a kare ta, idan kuma ta faru ya za’a yi maganin ta.

Haka kuma can cikin Kunkumin mata akwai mahaifa haka na ɗamiji ma akwai wurin da maraina suke, waɗannan duka masu maganin gargajiyar Afirika sun karance su kuma fahimci ɗabi’unsu. Wannan ɗabi’ar sanyi wancan ɗabi’arsa zafi.

 

A ƙarshe me dakta ke fatan isar wa a ƙarshen wannan tsari idan ya kai gaci?

Alhamdulillahi muna fatan samar da daftarin da za’a ɗora maganin gargajiya a kai, mu sake assasa wani wuri da za mu fara rubuta tarihin maganin gargajiyar Afirika, ba sauri mu ke ba ni ma bazan iya duka ba, tare za mu haɗu mu gina wannan aikin alhairi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Rubutu Da Marubuta: LOKACIN RUBUTU

Next Post

Dalilin Fim Na Koyi Harshen Hausa – Amina Amal

RelatedPosts

Har Yanzu Babu Sabuwar Kwalta Ko Kwalbati A Garin Giwa – Kwamred Alkurkawee

Har Yanzu Babu Sabuwar Kwalta Ko Kwalbati A Garin Giwa – Kwamred Alkurkawee

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Idris Umar Game da more romon dimukradiyya da wasu...

Zaman Lafiya

Marasa Son Tabbatuwar Zaman Lafiya A Nijeriya Ke Sukar Furucin Gwamna Bala Kan Fulani, Inji Ladan Salihu

by Muhammad
2 weeks ago
0

DAKTA LADAN SALIHU Shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar...

Cigaba

Mun Samar Da Daftarin Cigaba Na Shekara 10 Ne Domin Kafa Harsashin Inganta Rayuwar Gombawa –Gwamna Inuwa

by Muhammad
2 weeks ago
0

ALHAJI MUHAMMAD INUWA YAHAYA Shine gwamnan jihar Gombe, a wani hira ...

Next Post

Dalilin Fim Na Koyi Harshen Hausa – Amina Amal

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version