Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ta yi watsi da rahoton da aka buga a shafukan sada zumunta kan gano wasu malaman bogi da ke aiki a jami’ar.
BUK ta bayyana labarin a matsayin mara tushe..
- Bayan Ganawa Da Mohammed Bello Koko, Ma’aikatan NPA Sun Janye Shiga Yajin Aiki
- Mutum 6 Sun Kone, 4 Sun Jikkata A Harin Boko Haram A Borno
Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano ya ce, “Babu gaskiya a ikirarin gano irin wadannan malaman bogi da ke aiki a BUK.
“A ingantaccen tsarin koyo namu, wanda za a iya tabbatar da shi a duniya Jami’armu na kan gaba a duniya.
“Saboda haka hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero, Kano na fatan jawo hankalin jama’a cewa babu malaman bogi a ma’aikatan jami’ar ba ne.”
Farfesa Sagir, ya ce akwai bukatar mutane suke tantance sahihancin labari kafin amfani da shi.
Kazalika ya ce jami’ar za ta dauki matakin shari’a a kan masu son bata wa Jami’ar suna.