Biyo bayan jita-jitan mutuwar gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, a ranar Asabar, Gwamnatin jihar ta bukaci jama’an jihar da su yi watsi da wanan jita-jitar tare da cewa Gwamnan yana raye.
Ana ta samun tashin hankali dai a jihar sakamakon kokonton da jama’a ke yi na cewar ina gwamnan yake tun lokacin da ya dawo dag hutun shekara.
- Shugaban Eritrea Da Takwaransa Na Congo Kinshasa Sun Yabawa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
- Bello Matawalle Ya Wawashe Kudi Da Motocin Gwamnati — Gwamnatin Zamfara
Babbar jam’iyyar adawa a jihar, PDP ta fito a ranar Asabar din ta bukaci wadanda suka boye gwamnan da su fito su bayyana wa jama’a ina gwamnan yake domin toshe kafar jita-jitan.
A sanarwar manema labarai da jami’an watsa labarai na jam’iyyar a jihar, Kennedy Ikantu Peretei, ya fitar, PDP ta, “Tun bayan da wasu kafafe suka yada labarin da ke cewa Gwamnan ya shiga mayuwacin hali na rashin lafiyar da ba ya iya gudanar da aikinsa, hakan ya jefa jama’a cikin damuwa wanda a ta hakan ne aka yada cewa kila ma ya mutu.
“Gwamnan bai dawo ofis don cigaba da aiki ba tun lokacin da hutunsa na shekara ya kare a watan March. Ko wajen bikin kaddamar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba a gano Akeredolu ba.
“Don haka gwamnati ta fito ta mana da al’umma cikakken bayanin Ina we gwamnan yake Kuma a wani hali yake,” jam’iyyar ta shaida.
Sai dai, a martanin da kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Bamidele Ademola-Olateju, ya yi, ya ce, gwamnan na halartar dukkanin wasu manyan ayyukan gwamnati da suka zama dole.
Olateju ya ce, “An yi ta lafta mana kiran waya da sakonnin cewa wai gwamnan Jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, CON ya mutu.
“Mun so mu yi watsi da wannan kiran har sai da muka ga an kokarin siyasantar da lamarin da wawantar da hankalin jama’a.
“Muna sanar da jama’a cewa Gwamnan yana raye, su yi watsi da duk wata jita-jitan mutuwarsa,” ya shaida