Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta karyata rade-raden da wasu ke yi cewa, ta sanya ranar jarrabawa a ranar Idin Babbar Sallah.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a, Mista Azeez Sani, ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Ya ce majalisar tana sane da muhimmancin bukukuwan addini, don haka a ko da yaushe ta kan ware ranakun hutu wajen tsara Jadawalin jarrabawa.
“Hukumar ta Ware mako guda na hutun bukukuwan Sallah ga masu zana Jarrabawar kammala makarantar Sakandire, hutun ya fara ne daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Yuli, 2022.
“An yi hakan ne don baiwa Musulmai masu zana Jarrabawar damar gudanar da bikin Sallar Idi Babba,” in ji shi.