Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ba a biya kuɗin fansa ba kafin a ceto tsohon shugaban NYSC, Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya), daga hannun ‘yan bindiga.
A wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ya bayyana cewa an yi amfani da bayanan sirri da kuma dabarun soji wajen ceto Janar Tsiga.
- Dole Dukkanin Masu Umrah Su Fice Daga Saudiyya Kafin 29 Ga Afrilu – Hukumomi
- An Buɗe Sabbin Cibiyoyin Kula Da Masu Cutar Sankarau A Jihohi 6
An yi garkuwa da shi ne a mahaifarsa Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, ranar 5 ga watan Fabrairu, tare da wasu mutane 13.
Sojoji sun gudanar da samame a yankunan Ɗanmusa, Faskari da Kankara, inda ake tunanin ‘yan bindigar ke ɓuya, har suka samu nasarar ceto shi ba tare da biyan fansa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp