Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, ya ce har yanzu bai yanke shawara kan matakin da babban daraktanta, Doyin Okupe ya dauka na yin murabus daga mukaminsa ba.
Okupe dai ya mika takardar murabus dinsa ga dan takarar jam’iyyar, Peter Obi biyo bayan hukuncin da aka yanke masa a gaban kotu kan karya dokar halatta kudaden haram.
- Yadda Zan Inganta Rayuwar Talakawan Gombe- Mailantarki Na NNPP
- Za A Fara Rijistar Shiga Makarantun Gaba Da Sakandire UTME 14 Ga Janairun 2023 —JAMB
Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke wa Okupe hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari kan laifin karkatar da kudi.
Shugaban kamfen din ya fada a ranar Talata cikin wasikar murabus dinsa cewa lokaci ya yi da ya kamata ya ajiye mukaminsa amma ya ce goyon bayansa ga Obi har ya kai ga nasara a 2023.
Sai dai babban mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben, Tanko Yunusa a wata hira da gidan talabijin na Channels, ya ce kwamitin zai gana kafin ya yi wani bayani kan murabus din Okupe.
A cewarsa, mutum ba zai iya daukar irin wannan matakin ba yana mai dagewa cewa kwamitin zai yi taro ya dauki matakin gamayya wanda zai zama maslaha ga dukkan ‘yan Nijeriya.
Ya ce, “Ba mu fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da murabus din Dakta Doyin Okupe ba har sai kwamitin yakin neman zaben ya yi taro ya yanke shawarar abin da za a yi da kuma yadda za a yi.
“Don haka wadannan labaran na iya zama hasashe har sai kwamitin kamfen ya yi taro. Mu ba mutane masu zaman kansu ba ne inda mutum daya zai iya yanke hukunci Za a yanke shawara ne domin maslahar al’ummar Nijeriya”.