Idris Aliyu Daudawa" />

Babu Matsi Da Takurawar Da Zai Hana Atiku Zuwa Kotu —CUPP

Ranar litinin ce gamaiyar jam’iyyun siyasa a karkashin (United Political Parties) suka yi zargin cewar jami’an gwamnatin tarayya, suna yin taro da wasu jam’iyyun siyasa da kuma ‘yan takararsu na Shugaban kasa cewar, da niyyar su sa baki dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya amince da sakamakon zaben Shugaban kasa wanda aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu na wannan shekara.
An bayyana cewar su jami’an gwamnati a karkashin shugabancin Minista suna amincea madadin fadar Shugaban kasa cewar, ko wanne dan takara za’a ba shi Naira miliyan 40, bayan nan kuma za su kira taron ‘yan jaridu, inda gaba dayan su za su yi kira da Atiku Abubakar da yarda cewar ya fadi zabe, ba zai kia kara zuwa Kotu ba.
Mai magana da yawun kungiyar Imo Ugochinyere ya bayyana hakan, a cikin bayanin da aka rarraba wa manema labarai a Abuja.
Ugochinyere ya kara bayyana cewar shi Ministan tuni ya yi tarurruka da dama da su Shugabannin jam’iyyun, sakatarorinsu da kuma su ‘yan takarar Shugaban kasar .
Ya ci gaba da bayanin cewar, “ Gwamnatin tarayya zata tafka babban kuskure wajen kashe kudade, wadanda za su yi amfani da su wajen kiran taron ‘yan jarida, wanda a lokacin ne za su yi kira da Atiku Abubakar, da kuma jam’iyyar PDP, su yarda da cewar an kada su zabe, don haka kada su je kotiu su kalubalanci sakamakon wanda Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana.
“Idan har gaskiya ne sun amince da kuma yarda cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci zaben, kamar dai yadda suke son duniya ta sani, me yasa hankalinsu ya tashi, har kuma suna nem,an yin amfani da jam’iyyun siyasa, da su lallashi Atiku ya manta da maganar zuwa Kotu.
“Muna sanarwa mu babu wani abin da zai tayar mana da hankali, ko dai su jam’iyuyun siyasa wadanda ake son ayi amfani dasu, ko kuma wata kungiya, sai ‘dan takarar Shugaban kasarmu ya canza ra’ayin shi.
“ Su kuma jam’iyun siyasa wadanda suka yanke shawarar za su dadada ma wasu rai saboda wani dan abin da ba zai kai su wani wuri ba, ya kamata su gane cewar, duk mun san abin da suke yi, haka nan kuma tarihi ba zai yafe masu ba, idan har suka yanke shawarar za su timaka ma makiyan damukuradiyya, saboda a hana mutane abin da suka zaba..
“Da yake basu samu sa’ar abin da suka so yi ba, wajen yin hayar wasu mata a babban birni tarayya, wadanda za su yi jerin gwano akan layuka su ce bai kamata Atiku ya je kotiu ba, wani matakin da suka gaba kuma shi ne su samu ‘yan takarar Shugaban kasa.”
ma Atiku
Ya ci gaba da bayanin cewar, “Muna son yin kira da fadar Shugaban kasa da duk sauran wadanda suke taimaka masu, cewar Atiku Abubakar ba zai yarda da kuma amince ba, ya ki amsa kiran da al’ummar Nijeriya suka yi ma shi ba, ba wata barazana, ko kuma takurawa da zata sa ya ji tsoro ya ce ya fasa zuwa kotun.
“Don haka muna yin kira da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, daya daina yin wasu abubuwan da ya san ba zai samu goyon bayan al’ummar Nijeriya ba, domin yana son ya ci gaba da dorewa kan karagar mulki, duk wadannan abubuwan ba za su taimaka ma shi ba, saboda kuwa shi Atiku zai je Kotu ne ya kalu balance al’amarin na ita Hukumar zabe mai zaman kanta, a kotun sauraren kararrakin zabe na Shugaban kasa.
“ Mu har yanzu ma abin yana bamu mamaki da har yadda shi Shugaban kasa zai rika maganar cewar ya samu nasara a zabe, ta bangare daya kuma yana kai gwauro da mari wajen neman kada akai kara kotu, a yarda da shi sakamakon zaben.
“Sai dai kluma kash! ai ya riga makaro saboda shi jirgin na adalci tuni ya tashi daga tasha, saboda akwai kwararan shedu da suke nuna cewar shi Shugaban kasa yana kan kujerar da bata dace da shi ba, wannan ikkta ce manufar Atiku Abubakar.”

Exit mobile version