Ministan Sufuri, Mua’zu Jaji Sambo, ya ce kawo yanzu babu wata takamaiman ranar da za a dawo da sufurin jirgin Kasan Abuja zuwa Kaduna, wanda aka dakatar bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai masa a ranar 28 ga watan Maris, 2022.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci tashoshin Jirgin na Idu da Kubwa da ke Abuja, ya ce dole ne a sako dukkan fasinjojin da akayi garkuwa dasu kafin jirgin ya cigaba da jigila.
Ministan ya kuma ce, za a sanya duk wasu kayan sa’ido na aikin tsaro da ake bukata domin dakile duk wata barazanar tsaro a nan gaba kafin jirgin ya koma aiki.
Ministan ya ce, “Yana da matukar muhimmanci a fara kubutar da fasinjojin Jirgin da akayi garkuwa da su, a sake hada su da iyalansu, idan ba haka ba, za a ga gwamnati ba ta da hankali, amma gwamnati na yin duk abin da za ta iya don tabbatar da an kubutar da fasinjojin.
“ina ganin, fara hakan abu ne mai muhimmanci sosai da yafi da cewa.”