Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce matsalar durƙushewar babban layin wutar lantarki na Nkjeriya na iya ci gaba, musamman saboda lalacewar layin Shiroro-Kaduna-Mando da rashin tsaro ya haddasa.
Da yake magana a wajen kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa a Majalisar Dattawa, Adelabu ya bayyana cewa layin, wanda yake ɗaya daga cikin manyan hanyoyin kai wuta zuwa Arewacin Nijeriya, ya lalace tun watan Oktoba 2024 kuma har yanzu ba a gyara shi ba.
- Abubuwan Dake Kunshe Cikin Rahoton Shekara-Shekara Game Da Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin
- Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Ɓangaren Bafarawa Kan Rikicin Shugabannin PDP A Sakkwato
Ya ce matsalar ta haifar da ƙarin matsin lamba kan sauran layukan lantarki, wanda ke janyo yawan durƙushewar wutar.
Duk da haka, ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki don rage yawan faruwar matsalar tare da gyara layin nan ba da daɗewa ba.