Babban bankin Nijeriya (CBN) ya karyata ikirarin da wasu ke yi na cewa bankin zai sauya fasalin takardar Naira a watan Janairun 2024.
Bankin ya karyata ikirarin ne a cikin sanarwar da daraktan sashen sadarwa ba bankin Isa AbdulMumin ya fitar a yau Talata.
- Hukumar ‘Yansanda Ta Tabbatar Egbetokun A Matsayin Sufeto-Janar Na ‘Yansanda
- Kotu Ta Yanke Wa ‘Yan Daudu 8 Hukuncin Daurin Watanni 3 A Kano
Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa, wannan ikirarin karya ce da wasu ke yada wa don kawai su karkatar da tunanin ‘yan Nijeriya.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, a yanzu bankin bai da wani shirin sake fasalin takardun Naira, inda sanarwar ta shawarci ‘yan kasar da su yi watsi da wannan ikirarin da wasu ke yadawa na maganar sauya Naira.
A 2022 ne dai, CBN ya sauya fasalin takardun kudin na Naira 200, Naira 500 da kuma Naira 1000.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp