• English
  • Business News
Sunday, September 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babu Wanda Ya Jawo Ra’ayina  Zuwa Masana’antar Kannywood —Umar Hassan (2)

by Rabi'at Sidi Bala
2 hours ago
in Nishadi
0
Kannywood
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafi ne da ya saba zaƙulo muku fitattun jarumai, manya da ƙanana har ma da mawaƙa, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wani baƙon na musamman. Jarumi kuma mawaƙi, kana Malami mahaddacin Alƙur’ani mai gabatar da Tafsiri, wato UMAR HASSAN SAHIBUL ƘUR’AN Wanda aka fi sani da MAI FARIN JINI/GWANI UMAR. Inda ya warwarewa masu karatu zare da abawa game da abin da ya shafi harkar fim ɗinsa, da irin ƙalubalen rayuwar da ya fuskanta ta dalilin shigarsa masana’antar Kannywood, har ma da wasu batutuwan masu yawa.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da wanne fim ka fara, kuma ya farkon farawar ta kasance?

Fim ɗin dana fara fitowa na farko da na biyu gaskiya har yanzu ba su fita ba, sai dai na baya-bayansu. Kuma na farko an sha dabi, dan lokacin kawai abun aks saka a rai, amma ban san me ake nufi da ‘white shot’ ba, ban san me ake nufi da ‘See you’ ba, ban san me ake nufi da ‘Medium’ ba. Tsayuwar ma yadda zan yi sai na tsaya ma na kalli ‘Camera’ lokacin. A hankali tunda ana gani kuma an saka a rai za a yi, Allah kuma ya taimaka aka gane aka ɗau hannu. Dan yanzu idan zan yi fim ba a maimaita min ‘scene’ da an faɗa sau ɗaya shikkenan. Wani lokaci ma tunda abu ne na addini kawai in aka faɗa min ga abin da ake so na yi, duk sauran to, ni zan yi.

  • Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya
  • Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

Ko za ka iya tuna adadin finafinan da ka fito ciki?

Labarai Masu Nasaba

Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka.

Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo?

Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani hoto da muka yi ni da Maryam bodyguard a wajen bikin Abdul M. Shareef, wanda na je na buɗe da addu’a. Mun haɗu mun gaisa muka yi hoton, sai mutane suka yi ‘scrolling’ ɗin gurin, aka ce wai na taɓa ƙirjinta. Kuma ni riƙe hannu dake shiga tsakanin jarumi da jaruma ni bai taɓa haɗa ni da kowacce jaruma ba, balle har a ce ni na taɓa ƙirjinta. To, kuma ni na rasa inda zan taɓa ƙirjinta sai a cikin mutane, to a wannan na fuskanci ƙalubale sosai dan na zagu a social media.

Ka canza shawarar barin harkar ta dalilin hakan, ko kuwa ka kalli hakan matsayin jarrabawa tunda ka san baka yi ba?

Gaskiya a lokacin har furta cewa na yi na daina, daga baya ne mahaifiyata bayan ta riƙa ganin irin bidiyoyin, tunda daman da bidiyoyin waƙa na fara, sai ta bani shawarar ko zan yi na juyar da abin tunda ina so na mayar da shi ta wancen ‘part’ ɗin zai fi alkairi, shi ne na koma.

Ba ka ganin za a iya samun ƙalubale game da hakan, musamman yadda aka taɓo ɓangarori daban-daban, duba da yadda a yanzu ake samun rashin jituwa ga wasu malaman ta fannin bambancin Aƙida?

Dan matsala za a iya samun matsala, dalili kuwa shi ne, rigar malamai za a shiga. Sannan kuma abu ne da zai taɓa ɗari’a, izala, shi’a, dole wasu za su ga kamar za a ci mutuncinsu ne. Tunda ba a taɓa samun fim da ya haɗa wannan ra’ayoyin ace zai yi magana akan aƙidun nan gabakiɗaya ba za a samu wannan matsalar. Sai dai kawai abin da nake tunani ba dole su jagororin malamai su fahimta ba, in Allah ya sa su masu kallo da ake yi wa suka fahimci saƙon dake ciki buƙata ta biya. Kuma ni a shirye nake da zagi ko cin mutunci, ko mutuwa, ko ɗauri, akan wannan fim ɗin, matuƙar al’ummar musulmi sun fahimci abin da ake son su fahimta. Kuma ni bana jin ɗar-ɗar akan wannan fim ɗin duk zugar al’ummar duniya ina da yaƙini tunda gaskiya na sa a raina, kuma da manufa ce mai kyau Allah zai taimake ni ya yi mana jagoranci akan wannan fim ɗin.

Ka yi maganar ajjiye harkar fim, kenan kana ganin za ka iya ajjiye harkar fim gabaɗaya da zarar fim ɗin ya fita?

E! ina kyautata zaton hakan. Domin wannan shi ne burina wanda ya rage min a harkar fim, idan wannan fim ɗin ya fita ina kyautata zaton zan iya ajjiye harkar fim a gaba in sha Allah. Tsakanina da ita sai dai in bayar da shawarwari ko kuma in zan zama furodusa ko Darakta, amma dai aktin zan ja baya da shi, in sha Allahu Ta’ala. Shi ya sa ma ban fito na bayyanawa duniya ba. Dan akwai ‘Show’ ɗin Hadiza Gabon ta gayyace ni kuma a kan wannan gaɓar ne to, amma na jinkirta ban je ba saboda ina son lokacin da aka gama fim ɗin aka sake shi, zan furta cewa na daina fim in sha Allah.

Ko akwai wani fim da ya taɓa baka wahala a yayin ɗaukar shirin?

Babu wani fim da ya taɓa ba ni wahala, tunda mafiya yawanci duk abin da za a faɗa kwakwalwata ta saba ɗaukewa. Kuma rol ɗin da nake taka rawa ɗabi’a ta ce ta gaske ta almajirai, na kan zauna gaban dubunnan al’umma na ja musu na fassara musu. Saboda haka ko da na zo ‘camera’ ba ta zame min baƙon abu ba, kawai dai kafin na fahimci yadda ɗaukar ‘see you’ da ‘white shot’ ne ya ɗan wahalar da ni. Amma tunda na fahimta da riƙe ‘dialogue’ da yin ‘acting’ ba ya wahalar da ni.

Wane irin nasarori ka samu game da fim?

E! to, tunda dai har yanzu fuskata ba ta fashe ba, na ɗaukar hoto ne idan an ganni a gaske ace za mu yi hoto. Amma nasara da za a ce na kuɗi ko na mene duk abin da zan samu da bazar alƙur’ani nake samu. Ba zan ce ga wani abu guda ɗaya da fim ya yi min da zan yi alfahari da shi ba, kamar yadda zan danganta riga ta addini ta min. Ko dan na shiga da ƙafar hagu ne, ko kuwa baki ne na mutane da suka yi yawa ba sa sona da harkar na ƙaƙabe sai nayi. Hana ƙarya sau ɗaya watarana na hau mota daga wani waje wayata ta faɗi kuma ban tafi da ATM Card ba, muka haɗu da wani a mota ya ganni na dai hau motar ne ban ma san yadda zan yi ba, kawai in na sauka duk yadda za a yi sai a yi kawai ya ce “Wane kamar na sanka a fim’  na ce “Eh”. Muka fara surutu muna sauka ya biya min kuɗin mota to, sai na ji daɗi. Ni ba abin da zan ce fim ya yi min duk abin da za a ban a cikinsa gaskiya na fi ƙarfinshi, ni ba a taɓa bani kyauta a fim da ta fi ƙarfin wadata ta ba.

Ya ka ɗauki fim a wajenka?

Ni gaskiya ban ɗauki fim sana’a ba na dai ɗauki fim hanyar isar da saƙo, kuma a cikinta idan Allah ya ga dama zai iya haɗa ka da wani da zai yi maka hanyar wani alkhairin. Ban ga abin da fim zai min ba ya shafe abin da Allah ya shafa min na ni’imar addini ba, na abubuwan da nake samu a addini. Fim bai taɓa yi min ba, kuma bana tunanin daga nan har duniya ta tashi wai fim zai mamaye abin da na samu a darajar addini ba.

Mu koma ga ɓangaren waƙa, kamar wacce irin waƙa ka ke yi?

A horewa da baiwa da Allah (SWT) ya ɗan hore ba wacce ba na yi, tun daga kan ta biki, siyasa, ta sarakai da sauransu an ɗan taɓa. Amma waƙar soyayya ma ba layina ba ce saboda ni ba masoyin bane bana soyayya gaskiya.

Ka yi waƙoƙi sun kai kamar guda nawa?

Mutum ba ya zurawa da yawa, amma a taƙaice zan iya cewa sun kai kamar guda Talatin. A cikin waƙoƙin kuma akwai wacce na yi wa Hadiza Gabon wacce na bayar da labarin soyayyar da nake yi mata, duk da ita ma ƴ an jaridu sun sha yi min tambayoyi akan waƙar. Na yi mata waƙoƙi guda goma.

Waɗanne irin tambayoyi aka fi yi maka game da waƙar, kuma ya karɓuwar waƙar ta kasance ga Hadiza Gabon ɗin?

Wasu na tambaya ta, shin soyayyar da na yi mata a waƙar so ne na aure ko so ne na ‘fans’?. Saboda waƙar na yi ta ne me harshen damo, sannan na bayyana ƙalubalen da na fuskanta wajen neman ganinta a cikin waƙar. To, wasu sun kikkira har a gidajen radiyo, shin ƙalubalen dana fuskanta gaske ne ko ba haka bane?. Sannan ita kanta ta san da waƙar amma a lokacin ban wani samu karɓuwa a wajenta ba, saboda wataƙil tunaninta irin mutanen nan ne da suke zuwa da salo domin su sami kuɗi. A iya tunaninta kamar na yi ne domin na samu kuɗi, kuma a lokacin da rufin asirina ba na tunanin za ta yi min wani abu.

Ka iya waƙa sai dai kuma ba ka saka sunanka akan waƙarka, me ya sa hakan?

Mafiya yawancin waƙoƙina ba na saka sunana dukka waƙoƙina haka suke, da na fara sakawa amma kuma da na fahimci ba a so ni ma kuma bana son na bayyanar da kaina sai na riƙa ɓoye sunana. ‘Studio’ da na y waƙa sai na saka sunan, misali idan na yi a Munnir Ali to, za ki ga an saka Munir Ali, haka idan a ‘studio’ Auta mg ne za a saka ‘Mg Boy Record’. Sai ka shiga za ka ji muryar ba ta shi ba ce, tawa ce. Ko na Umar M. Sharif ne zan sa a saka sunan ‘Studio’ ɗinsu, da dai sauransu.

Ba ka gudun a sace maka waƙa?

Sacewa an daɗe ana sacewa, amma ni bai taɓa damuna ba. Dan akwai wata waƙa da na taɓa yi ban taɓa jin an juya ta waƙar ba, sai da na je birnin kebbi, watarana zan je Nijar kawai na ji an saka ta ana ‘Campaign’ da ita. Wallahi waƙar da karin da baitin duk tawa ce, kuma na san mawaƙin ‘studio’ da na je na yi waƙa a ciki shi ya juya waƙar ya yi wa wani. Amma ni bai taɓa damuna ba gaskiya, saboda a ɗauki ma abun ka a juya alamu ne na an yaba da baiwarka, dan da ba da baiwar taka ba wani ko kaya ba zai sata ba.

Waɗanne Jarumai ne suke burgeka kafin ka fara fim, da kuma bayan shigar ka?

Ali Rabi’u Ali Daddy, sai Nura Hussain, su biyun nan su suka fi burge ni. A mata kuma jarumar da ta fi burge ni su uku ne, ta farko akwai Hadiza Gabon, sai jaruma ta biyu Zainab Basarakiya, sai ɗaya jarumar tana masifar burge ni, sai dai yadda na ɗauke ta ita ba haka ta ɗauke ni ba, shi ya sa ma ba zan ambaci sunanta ba.

Wane ne ubangidanka a masana’antar Kannywood?

Idan na ce babu ban yi biyayya ba, idan kuma na ce akwai na yi ƙarya. Zan dai iya cewa iya da ‘role model’ Ali Rabi’u Ali Daddy, kuma idan zan kira Ubangida ma shi ne ubangidana. Da ni da Aminu Saira me Labarina, da irinsu Salisu S. Fulani, da Sahabi Kwana Casa’in, da su Mudassir Isyaku Dutsenma, duk shi ne maigidanmu da sauransu. Dan a maza cikin Kannywood, ba a yi wanda nake so kamar shi ba.

Ko kana da waɗanda za ka gaisar?

A ƴ an fim zan yi musu jimlatan gabakiɗaya ina gaida kowa da kowa fatan alkhairi, Allah ta’ala ya cikawa kowa burinsa na alkhairi.

Muna godiya

Ni ma na gode.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Jarumar Fina-finan KannywoodKannywood
ShareTweetSendShare
Previous Post

Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan Arsenal Da Manchester City 

Next Post

Komai Nisan Dare Gari Zai Waye

Related

Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan
Nishadi

Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan

7 days ago
Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango
Nishadi

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

1 week ago
Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)
Nishadi

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

2 weeks ago
Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba
Nishadi

Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

3 weeks ago
Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah
Nishadi

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

4 weeks ago
Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya
Nishadi

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

1 month ago
Next Post
Komai Nisan Dare Gari Zai Waye

Komai Nisan Dare Gari Zai Waye

LABARAI MASU NASABA

SERAP, Amnesty Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Kan Sowore, X Da Facebook

SERAP, Amnesty Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Kan Sowore, X Da Facebook

September 21, 2025
Komai Nisan Dare Gari Zai Waye

Komai Nisan Dare Gari Zai Waye

September 21, 2025
Kannywood

Babu Wanda Ya Jawo Ra’ayina  Zuwa Masana’antar Kannywood —Umar Hassan (2)

September 21, 2025
Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan Arsenal Da Manchester City 

Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan Arsenal Da Manchester City 

September 21, 2025
Ko Ka San Dalilin Da Zai Bai Wa Nijeriya Damar Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?

Ko Ka San Dalilin Da Zai Bai Wa Nijeriya Damar Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?

September 21, 2025
Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku

2027: ‘Ku Yi Zaɓe Bisa Ga Ra’ayin Kanku, Ba Lura Da Ƙabila Ko Yanki Ba’, – Atiku Ga ‘Yan Nijeriya

September 21, 2025
Kannywood

An Cafke Wani Magidanci Da Lafin Sojan Gona A Katsina

September 21, 2025
Kannywood

Wata Mahanga Ta Daban Ta Kallon Ayyukan Ta’addanci

September 21, 2025
Gwamna Lawal Ya Raba Kayan Karatu 408,137 Ga Makarantun Gwamnatin Zamfara

Gwamna Lawal Ya Raba Kayan Karatu 408,137 Ga Makarantun Gwamnatin Zamfara

September 21, 2025
Ko Ƙasashen Musulmi Za Su Iya Kafa Ƙawancen Tsaro Don Tunkarar Abokan Gaba?

Ko Ƙasashen Musulmi Za Su Iya Kafa Ƙawancen Tsaro Don Tunkarar Abokan Gaba?

September 21, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.