Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa babu wata ƙaramar hukuma a cikin jihar da ƴan ta’adda ko ƴan bindiga ke da iko da ita. Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka gudanar a sabon gidan gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a ranar Talata.
Gwamna Mutfwang ya ce gwamnatinsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro, musamman ta hanyar farfaɗo da rundunar tsaron cikin gida ta jihar wato Operation Rainbow, domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
- Ana Ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Malam Adamu Fika
- Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A Filato
Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an dawo da zaman lafiya a sassan jihar da rikice-rikicen ƙabilanci ko na addini suka taɓa. Ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya domin tabbatar da fahimtar juna da daidaiton al’umma.
Gwamnan ya sake jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya. Ya ce kafa ƴansandan jiha zai bai wa gwamnatocin jihohi damar yin tsari da ɗaukar matakan da suka dace da yanayin tsaron yankunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp