Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya karyata raɗe-raɗin da ake yaɗawa a baya-bayan nan cewa, ya cimma yarjejeniya da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP.
A wata hira da BBC, Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya ce bai san da irin wannan yarjejeniyar ba, amma ya ji labarin cewa, magoya bayan Atiku na ganawa da shugabannin al’umma da suka hada da malamai domin yada wannan farfagandar.
- Wata Gidauniyar Kasar Sin Ta Mika Ma’ajiyar Ruwa Ga Al’ummar Wani Kauyen Habasha
- Gwamnatin Sakkwato Ta Kaddamar Da Gangamin Sa Yara A Makaranta
Ya ce: “Wannan labarin ya sosa min rai matuka, inda na ji cewa, dattawa na yaɗa ƙarya game da abin da bai faru ba. An gaya min cewa, kusan malamai 45 ne aka tara aka sanar da su wannan kage-kagen labarin. Ko kaɗan ban ji daɗin hakan ba.
“An gaya musu, na amince da yarjejeniyar cewa, Atiku zai yi shekara huɗu, zan yi shekara huɗu, Peter Obi kuma zai yi shekara takwas a kan mulki. Wannan gaba ɗaya karya ne; irin wannan yarjejeniya sam ba bu ita.”
Kwankwaso ya bayyana cewa, tun da ya bar PDP ya koma NNPP ya samu kwanciyar hankali tare da nesanta kansa da abin da ya bayyana a matsayin wulakanci da shi da magoya bayansa suka fuskanta a PDP.