Daga Mustapha Hamid, Abuja
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗa wa a kafafen watsa labarai na cewa, zai fuskanci kwamitin da majalisar wakilai ta kafa domin bin diddigin yadda asibitin fadar shugaban ƙasa ya kashe kuɗaɗen da aka ware masa tun daga shekarar 2015.
Ya bayyana cewa, ba shi da wata alaƙa ta kusa ko nesa da kasafin kuɗin shekarar 2015, kafin ya miƙa ragamar mulki ga Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun 2015.
Tsohon Shugaban Ƙasan ya bayyana haka ne a wata takardar manema labarai, wacce ta fito daga mai magana da yawunsa, Mista Ikechukwu Eze a shekaran jiya Asabar a Babban Birnin Tarayya Abuja.
“Majalisar dattawa a ranar Alhamis 12 ga watan Oktoban 2017 ta cimma matsayar cewa za ta binciki kuɗaɗen da aka ware wa asibitin fadar shugaban ƙasa, wanda kuma wasu kafafen yaɗa labarai suke ta ƙoƙarin shafa wa tsohon shugaban ƙasa kashin kaji.
“A zaton mu, kafafen yaɗa labarai ne za su kasance a sahun farko wurin tuna wa ‘yan Nijeriya cewa a ranar 29 ga watan Mayun 2015 Jonathan ya bar ofis, wanda kuma bai da wata alaƙa ta kusa ko nesa da kasafin kuɗin wannan shekarar.
“Domin kawar da duk wani zargi, sanin kowa ne cewa kasafin kuɗin shekarar 2015, wanda majalisar ta zartas a watan Afrilu, an tabbatar da shi a matsayin doka ne a watan Mayun shekarar 2015.A dalilin haka, bisa sabbin sharuɗɗa da ƙa’idojin da suke ƙasa, babu ta yadda za a tuhumi Jonathan da zartas da kasafin kuɗin shekarar 2015, kafin ya bar fadar shugaban ƙasa a watan Mayun 2915.
Eze ya ƙara da cewa: “Bisa la’akari da yadda ake ta ƙoƙarin sai an shafa wa Jonathan kashin kaji. Abin ya koma tamkar tun bayan samun ‘yancin kai, har zuwa yau Jonathan ne ke mulkin Nijeriya. Duk abin da aka yayubo, sai a jibga mishi.