Jam’iyyar PDP ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa a binciki tsohon babban hafsan sojin kasa (COAS) kuma Ambasada a Jamhuriyar Benin, Laftanar-Janar Tukur Buratai (mai ritaya) kan almundahanar Naira Biliyan 1.8 na sayen makamai.
A cikin wata sanarwa da kakakinta, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta ce ya kamata a binciki Buratai kan zargin badakalar Naira Biliyan 1.8 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kwato a wasu kadarorin Abuja.
- Na Bai Wa Peter Obi Damar Zama Abokin Takarata – Kwankwaso
- Rashin Yaba Kwalliyar Mace Daga Mijinta: A Ina Gizo Yake Sakar?
PDP ta ce bukatar binciken Buratai ya ta’allaka ne kan ikirarin da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Babagana Monguno ya yi baya ficewar Janar Buratai a matsayin COAS na cewa dala biliyan 1 da aka karbo daga asusun kasa a karkashin jam’iyyar APC. Ba a iya gano yadda ake gudanar da sayan makaman yaki da ta’addanci ba.
Jam’iyyar ta ce wannan ikirari da hukumar ta NSA ta yi ya kara nuna shakku kan zargin wawure kudaden da ake son yi wa jami’an tsaronmu kayan aiki, inda ta kara da cewa “irin wannan cin hanci da rashawa a karkashin gwamnatin APC ya haifar da karuwar hare-haren ta’addanci ba tare da tangarda ba, da kashe-kashen jama’a da kuma asarar rayuka. da yawa daga cikin mayakanmu na gaba a cikin shekaru bakwai da suka gabata.”
Jam’iyyar adawar ta kuma ce rahotannin sace-sacen da shugabannin jam’iyyar APC da mukarrabansu ke yi a ma’aikatu da hukumomin gwamnati na kara tabbatar da cewa gwamnatin APC ta zama mafakar masu wawure dukiyar kasa.
“Bugu da kari, kwanan nan da aka fallasa wawure Naira biliyan 80 da Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya yi, wanda bincike ya yi sanyi a halin yanzu ana zargin jami’an gwamnatin APC ne suka kitsa wani abu a kai.
“Jam’iyyar PDP da ke tsaye ga ‘yan Nijeriya, ta bukaci Janar Buratai ya dawo kasar nan don ya fuskanci bincike domin ya wanke sunansa.
“Wannan shi ne saboda duk wani zargin da ya shafi wawure kudaden da ake nufi da yaki da ta’addanci yana da matukar muhimmanci ga kasar nan. Dole ne a yu bincike sosai kuma duk wanda aka samu yana da hannu ya fuskanci cikakken hukuncin doka, “in ji jam’iyyar.