• English
  • Business News
Monday, July 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Badaƙalar Kwangilar Sayen Magunguna A Kano: Da Wa Za Ta Bare?

by Abdullahi Muh'd Sheka and Sulaiman
11 months ago
in Labarai
0
Kano
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kamar yadda bayanai suka karade kafafen sada zumunta da dama kan batun badakalar kwangilar sayen maganguna ga kananan hukumomin Jihar Kano 44, wanda ya zama abin da ake ta cece-kuce a kansa, musamman ganin yadda shi jagoran gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf aka ji shi a wurin wani taro yana rantsuwa da Allah cewa duk wanda suka samu da hannu cikin kowacce irin badakala ba za su saurara masa ba. 

Cikin wadanda ake zargi na da hannu dumu-dumu har da dan’uwan jagoran Kwankwasiyya, Musa Garba Kwankwaso da kuma guda cikin makusancin gwamna wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi.

  • Kaico: Wata Mata Ta Bankawa Kanta Wuta A Jigawa
  • Sin Ta Zama Zakaran Gwajin Dafi A Fannin Goyon Bayan Zaman Lafiya Da Adalci Tsakanin Kasashen Duniya

Wannan bankado badakalar ta tayar da hankalin Gwamnatin Kano, inda aka ji gwamna a cikin wata tattaunawa da shi yana bayyana cewa ba shi da masaniyar wannan harkalla, har sai da mai kwarmaton nan mazaunin kasar China, Dan Bello ya fallasa lamarin, wanda hakan tasa Gwamna Abba shan alwashin gudanar da bincike kan al’amarin.

Labarai Masu Nasaba

Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano

Za A Fara Bayar Da Bashin Miliyan 10 Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu

Kamar yadda bayanai ke nunawa, an yi kokarin kanface naira miliyon Goma-goma daga asusun a jiyar kowacce karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar Kano 44, sannan ana ganin akwai sa hannu ko amincewar wasu kamar shugabannin kungiyar kananan hukumomin Jihar Kano, manyan daraktocin gudanarwar kananan hukumomi, daraktocin binciken ayyuka da tsare-tsaren kananan hukumomi, wanda ake ganin an kulla yadda aka yi amfani da kamfanin dan’uwan Kwankwaso, Garba Musa Kwankwaso mai suna ‘Nobomed Pharmaceuticals company.’

Babban abin da jama’a da sauran masu nazarin harkokin yau da kullum ke hange shi ne, shin an ya Hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado za ta iya gudanar da sahihin bincike da zai kai ga hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin wannan badakala, musamman ganin shi kansa shugaban hukumar da ke sauraron korafe-korafe ta kansa yake a halin yanzu, domin akwai korafe-korafe a kansa da ke gaban kotu.

Haka shi ma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Shehu Wada Sagagi wanda cikin makonnin da suka gabata wasu fusatattun matasa suka afka wa wata makaranta da aka ce mallakarsa ce tare gano shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar domin raba wa al’umma wanda a jibge cikin makarantar, wanda haka tasa Sagagin garzayawa kotun, inda ya samo umarnin hana kamashi ko ci gaba da bincikarsa.

Da yawa mutane a Kano na kallon Gwamnatin Abba a matsayin gwamnatin dangi da abokan arziki, domin nade-naden da ke kunshe a cikinta ya nuna wasu da yawa na da alaka ta kusa ko ma ta jini da jagororin tafiyar, musamman an ga yadda watannin kadan da suka gabata aka nada dan Sanata Kwankwaso a matsayin Kwamishina, sannan akwai wasu masu fada aji a fadar gidan jagoran na Kwankwasiyya wadda ake ganin taba su na da wahalar gaske.

Hakan tasa ake ganin ba wata rawar a zo a gani da hukumar Muhyi Magaji za ta iya takawa wajen hukunta wadanda ake zargin cikin wannan badakala.

A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ta wayar tarho a Kano ranar Talata, an ji Muhyi Magaji na cewa, “Mun fara bincike mai zurfi kan zarge-zargen da ake yi game da samar da magunguna na biliyoyin naira ga kananan hukumomi 44.

Ya ce, “Duk wanda ke da hannu, za mu gano shi kuma za mu hukunta wadanda aka samu da laifi.”

A cewarsa, hukumar na binciken zargin karkatar da kayan abinci da aka yi wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.

Kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye da Darakta Janar na yada labaran gwamna, Sanusi Dawakin-Tofa ne suka sanya hannu a kan sanarwar.

Don haka gwamnan ya umurci hukumar da ta gaggauta fara bincike kan lamarin tare da kai rahoton sakamakon domin daukar matakin da ya dace.

Yanzu dai abin da aka jira a gani shi ne, yadda za ta kasance tsakanin hukumar Muhyi wanda shi kansa ake ganin na kasu da gwamnatin Abba ne, kuma gashi aiki ya biyo takansu, sannan kuma shi kansa yana da matsala a gaban kotu, ga kuma rantsuwar da gwamna ya yi na alkawarin ba zai daga wa duk wanda aka samu da almundahana kafa ba.

A halin da ake dai, Hukumar karbar koke-koke da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, ta kama wasu mutane biyar da suka hada da Alhaji Mohammed Kabara, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, bisa zargin badakalar samar da magunguna na biliyoyin Naira.

Daga cikin wadanda aka kama akwai Garba Kwankwaso, Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Nobomed, wanda dan uwa ne ga Shugaban Jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnatin Kano Za Ta Tsara Zamantar Da Magungunan Gargajiya

Next Post

PCACC Ta Kama Shugabannin Ƙananan Hukumomi 3 Bisa Zargin Almundahanar Miliyan 660

Related

Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano
Labarai

Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano

20 minutes ago
Za A Fara Bayar Da Bashin Miliyan 10 Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu
Labarai

Za A Fara Bayar Da Bashin Miliyan 10 Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu

1 hour ago
An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar
Labarai

An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar

2 hours ago
Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya
Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya

4 hours ago
Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar
Labarai

Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar

14 hours ago
Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo
Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

15 hours ago
Next Post
PCACC Ta Kama Shugabannin Ƙananan Hukumomi 3 Bisa Zargin Almundahanar Miliyan 660

PCACC Ta Kama Shugabannin Ƙananan Hukumomi 3 Bisa Zargin Almundahanar Miliyan 660

LABARAI MASU NASABA

Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano

Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano

July 28, 2025
Za A Fara Bayar Da Bashin Miliyan 10 Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu

Za A Fara Bayar Da Bashin Miliyan 10 Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu

July 28, 2025
An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar

An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar

July 28, 2025
Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya

July 28, 2025
Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar

Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar

July 27, 2025
Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

July 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

July 27, 2025
Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

July 27, 2025
Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

July 27, 2025
Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

July 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.