Wata kungiyar magoya bayan Fc Barcelona mai suna ‘Sun Um Clam’ ta bukaci shugaban kungiyar, Joan Laporta akan ya yi murabus daga kan mukamin shi na shugabancin kungiyar bayan abinda suka kira gazawa da ya yi wajen yin rajistar sabbin yan wasa.
A lokacin bazara, Barcelona ta dauko dan wasan gaban kasar Sifaniya Dani Olmo daga kungiyar RB Leibzig ta kasar Jamus, amma tun wancan lokacin kungiyar ta gaza yi masa rajista a matsayin cikakken dan kwallonta, hakan ne yasa wasu ke ganin wannan a matsayin gazawa da sakaci daga bangaren shugaba Joan Laporta.
- Ɓaraka:, Ƴan Adawa, Shugabannin APC Na Shirya Kafa Sabuwar Tafiya — Lukman
- Gudummawar Sin Ga Aikin Samar Da Duniya Mai Tsafta Da Kyan Gani
Laporta ya maye gurbin tsohon shugaban Barcelona Joseph Maria Bortemeau, inda kuma ya yi alkawarin dawo da martabar kungiyar ta hanyar lashe manyan kofuna, sabunta filin wasa da kuma dauko manyan ‘yan wasa zuwa Camp Nou.
Amma tun bayan zuwansa, an samu karancin rajistar manyan ‘yan wasa, wanda daga ciki akwai Dani Olmo da Pau Victor wadanda a yanzu haka suke da yiwuwar barin Barcelona matukar ba a dauki mataki akan hakan ba.