Wata kungiyar siyasa da zamantakewa mai suna Arewa New Agenda (ANA), ta bayyana goyon bayanta ga sabon ministan tsaro da aka nada, Mohammed Badaru Abubakar, inda ta ce masu sukar nadin nasa ba su da masaniya kan kwarewar da yake da ita.
Shugaban kungiyar Sanata Ahmad Abubakar MoAllahyidi ne, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.
- Ana Zargin Gwamnatin Jihar Katsina Da Yin Rufa-Rufa Da Kudaden Ƙananan Hukumomi
- Rushewar Gini: Wike Ya Umarci A Cafko Mamallakin Ginin Cikin Gaggawa
LEADERDHIP ta ruwaito cewa, ANA ta yi hasashen yadda yankin Arewa zai ci gaba da habaka.
Yayin da sabbin ministocin suka shiga zama a ofisoshinsu, ANA ta nuna rashin jin dadinta kan abin da ta kira sukar rashin adalci da ake yi wa wasu Ministocin, wadanda wasu suka fake da rigar Addini da kabilanci wajen sukarsu.
MoAllahyidi ya ce: “Mohammed Abubakar Badaru, sabon ministan tsaro da aka nada, an ware shi ana sukarsa ba komai ba ne face rashin adalci.
“Shekaru takwas da Badaru ya yi a matsayin Gwamnan Jihar Jigawa abin koyi ne na tabbatar da tsaro, zaman lafiya, da zaman tare duk da raunin da jihar ke fama da shi.
“Duk da kasancewar jihar Jigawa makwabciyar kasashe da jihohi masu fama da rashin tsaro, jihar na daya daga cikin jahohin Arewa da ba su taba fuskantar matsalar rashin tsaro ba.
“Kungiyar ta ga ya dace ya jagoranci ma’aikatar tsaro, idan aka yi la’akari da tarihinsa na kare martabar yankinsa.
“Nasarar da Badaru ya samu a fagen jama’a da kuma na sirri ya nuna kwarewarsa kan wannan fage.”
ANA ta jaddada wajibcin samun goyon baya da mutunta shugabanci, inda ta yi watsi da duk wani kira na sauya Badaru daga mukamin ministan tsaro
MoAllahyidi ya kara da cewa: “ANA ta kuduri aniyar samar da zaman lafiya yayin da Najeriya ke ci gaba da kokarin inganta kasa.
“Babu shakka, Nijeriya tana cikin wani yanayi. Bukatar ministocin masu tunani da za su iya amfani da albarkatun dan Adam da na kayan aiki don inganta rayuwar ‘yan kasa.”
ANA ta taya ministoci 45 da aka rantsar a baya-bayan nan murna, sannan ta bukace su da su yi kokari wajen samar da bambamci, yana mai cewa nadin nasu ya ba da wata sabuwar dama ta ciyar al’umma gaba.
Sai dai ANA ta yi kira ga ministocin yankin Arewa da su yi aiki tukuru domin ci gaban Arewa da ma Nijeriya baki daya.
Kungiyar ta jaddada bukatar fifita hangen nesa fiye da bukatun kashin kai, inda ta bayyana manyan manufofin da shugaban kasa ya gindaya.
ANA ta jaddada muhimmancin ministocin da su yi hulda da jama’a don fahimtar bukatunsu tare da shigar da su cikin ajandar gwamnatin Shugaba Tinubu.