Umar Faruk" />

Bagudu Ya Kafa Kwamiti Kan COVID-19 A Kebbi

Gwamna Bagudu

A jiya Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya kafa kwamitin kwararun jami’an kiyon lafiya don samar da hanyoyin bada kariya da kuma fadakar wa  ga al’ummar jihar kan bular cutar coronabirus a wasu Jahohin kasar Najeriya da kuma kasashen Duniya baki daya.

Bayanin kafa kwamitin yana kunshe ne a wasu takardun gwamnatin jihar ta Kebbi da Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Babale Umar Yauri ya sanya wa hannu don bayyana wa manema labaru ta hannu Mai bawai Gwamna Abubakar Atiku Bagudu Shawara kan yada labaru Yahaya Sarki, inda takardun sun nuna cewar ” Kwamishinan ma’aikatar Kiyon Lafiya na jihar, Alhaji Muhammad Jafaru shine zai jagorancin Shugaban kwamitin sai Sakataren ma’aikatar Kiyon Lafiya zai kasance Babban Sakataren kwamitin”.
Sauran mambobbin kwamitin sun hada da Babban Sakataren ma’aikatar kananan hukumomin da masarautun gargaji, Babban Sakataren ma’aikatar Filaye da gidaje, Babban Sakataren ma’aikatar Yada labaru da al’adun, wakilai daga hukumar Lafiya ta Duniya wato ( World Health Organization)  wakilan Sarakunan gargajiyar na jihar da kuma Daraktan hukumar Bada agajin gaggawa ta jihar wato (State Emergency Management Agency) .
Haka kuma Sauran sun hada da shugaban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke a Birnin-Kebbi wato (chief Medical Director, federal Medical center), Babban Sakataren hukumar kula da kiyon lafiya na Asibitotin kananan hukumomin wato ( State Primary Healthcare Debelopment Agency) da kuma shugaban kungiyar Asibitotin kananan hukumomin na jihar.
Har ilayau mambobin Kwamitin sun hada da Daraktan Magungu, Shugaban kungiyar Shuwagabannin kananan hukumomin na jihar wato (ALGON chairman) Mataimakin Shugaban kula da barkewar curutoci na jihar, Daraktan kiyon lafiya, Hayatu Bawa daga fadar gwamnatin jihar, wakilan jami’an tsaro na ‘Yan sanda , DSS da kuma FRSC .  Kaza lika a cewar  takardun ” an daura wa Kwamitin nauyin gudanar na da yekuwa da fadakar wa kan bular cutar coronabirus ga al’ummar jihar ta Kebbi. Haka kuma da tabbatar da cewar ” dukkan matafiya da zasu shigo jihar ta filin jirgi ko ta iyakokin ta an gudanar da gwajin lafiyar su kafin shigo wa cikin jihar “.
Bugu da kari gwamnatin jihar ta Kebbi ta umurci Kwamitin dasu tabbatar da sun yi hada gwiwa da Babban Kwamiti na kasa da gwamnatin Tarayya ta kafa don bada kariya da kuma samar da hanyoyin magance matsalar cutar coronabirus ga al’ummar kasar Najeriya da kuma na sauran jahohin.
Daga nan kuma Kwamitin zasu rika bawai Gwamna Abubakar Atiku Bagudu bayyana yana yin yadda su ke gudanar da ayyukkansu da kuma nasarorin da suke samu na yau  da kullun.
Daga karshe gwamnatin jihar tana godiya ga irin kokarin da jami’an kiyon lafiya keyi ga fadakar da al’umma a jihar kan matakan da ya kamata su dauka don kariya ga kamuwa ga cutar Coronavirus a cikin jihar .

Exit mobile version