Ga alama dai mahukuntan Amurka, na ci gaba da aiwatar da mummunar manufar nan ta muzgunawa kamfanonin kasar Sin dake gudanar da halastattun ayyukan su bisa doka.
A baya bayan nan, gwamnatin Amurkan ta sake kakaba takunkumin cinikayya kan wasu kamfanonin Sin guda 5, wadanda ta zarga da cewa wai, suna taimakawa ayyukan soji da na tsaron kasar Rasha.
To sai dai kuma, tuni masu fashin baki suka fara bayyana rashin dacewar wannan mataki na gwamnatin Amurka, duba da cewa mataki mafi dacewa, shi ne mika wannan batu gaban kwamitin tsaro na MDD, wanda bisa doka, shi ne ke da alhakin tabbatar da ko wadannan kamfanoni sun cancanci a kakaba musu takunkumi ko a’a, amma ba wata kasa guda ta aiwatar da mataki bisa radin kan ta ba.
Ko shakka babu, Amurka na gwada wani irin misali ga sauran kasashe na rashin sanin ya kamata, da nuna karfin tuwo kan kamfanonin sauran kasashe ba tare da kiyaye dokokin kasa da kasa, da na cudanyar kasashen duniya ba.
A wannan gaba da Amurka ke yi kunnen uwar shegu, da kiraye-kiraye da Sin ke yi mata, na bukatar hawan teburin shawarwari domin warware sabani, ko ma duk wani nau’in rashin fahimta daka iya bijirowa, idan kasar Sin ta maida martani mai karfi, ya zama wajibi Amurka ta dauki alhakin tasirin hakan, a kan ta da ma al’ummar kasar sa, wadanda sau da yawa su ne ke dandana kudar mummunan tasirin da hakan ke haifarwa.
Ya kamata mahukuntan Amurka su lura da cewa, rashin jituwarsu da Rasha, ba zai zamo dalili na lalata halastacciyar alakar Rasha da sauran kasashen duniya ba.
Kuma har kullum kasar Sin na nacewa kan matsayin ta, na mai ingiza shawarwari da za su kai ga warware rikicin Ukraine cikin lumana, matakin da ya kamata Amurka ta nunawa yabo, maimakon kushe da nuna kiyayya. (Saminu Hassan)