Mataimakin Zaunannen Wakilin Sin da ke Majalisar Dinkin Duniya Dai Bing, ya bayyana a jiya cewa, yankin da kasar Iraki ke ciki yana da muhimmanci, ganin yadda ke kunshe da kabilu da mabiya addinai da dama, don haka ya kamata a mai da kasar a matsayin mai hade kan yankin da take ciki, a maimakon fagen takarar siyasa tsakanin bangarori daban-daban.
Dai Bing ya bayyana hakan ne a yayin da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya ke bincike kan batun kasar Iraki, inda ya ce kasar Sin ta ya ba wa Iraki bisa kokarin ta na sada zumunta, da sa kaimi ga hadin gwiwa a yankin da take ciki, kana ta nuna goyon bayan matakin kasashen Iraki da Kuwait, a aikin da suke yi na kokarin gano wasu ‘yan kasar Kuwait da suka ba ce, dama ido da dukiyoyin kasar Kuwait.
- Samar Da Ingantattun Bayanan Kidaya Sirri Ne Na Kyakkyawan Ci Gaba – Ganduje
- Bai Wa Hukumomin Alhazai Na Jihohi ‘Yanci Zai Taimaka Wajen Inganta Aikin Hajji – Barista Abdullahi
Ya ce Sin tana tsayawa tsayin daka, kan manufar kiyaye ikon mulkin kai, da cikakkun yankunan kasa ciki harda na kasar Iraki, tana kuma son ganin yadda ake kiyaye tsaro ta hanyar hadin gwiwa.
Dai Bing ya kara da cewa, a halin yanzu, kasar Iraki tana cikin lokaci mai muhimmanci a fannin siyasa, wanda cikin sa ake fuskantar manyan ayyuka, kamar kafa sabuwar gwamnati.
Don haka kasar Sin kefatan bangarori daban- daban na kasar Iraki, za su kara hadin gwiwa, da daidaita matsalolinsu, da cimma daidaito kan harkokin siyasa, ta hanyar yin shawarwari bisa kundin tsarin mulki da dokokin kasar, ta yadda za a kai ga aza tubalin siyasa, a kokarin samun zaman lafiya mai dorewa da bunkasuwa da wadata a kasar.
Ya ce ya kamata sassan kasa da kasa su girmama ikon mallakar yankunan kasar Iraki, su nuna goyon baya ga jama’ar kasar wajen zaben hanyoyin bunkasa kasarsu masu dacewa da yanayinta.