Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja, Ireti Kingibe, ta ce ya kamata jami’an gwamnati su rika amfani da motocin da aka hada a Nijeriya kadai.
Ta bayyana ra’ayinta da cewa, yin hakan zai shawo kan koke-koke da jama’a ke yi na tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arzikin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
Sanata Kingibe, ta bayyana hakan ne a wani shirin ‘Siyasar mu a yau’ a daren Laraba wanda gidan talabijin na Channels ke shirya wa. inda ta kara da cewa “ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba.”
Da aka tambaye ta, ko me za ta kawo sabo don shawo kan kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, Kingibe ta ce, “Zan nananta kudurina cewa duk motocin gwamnati a hada su a Nijeriya. Hakan zai taimaka matuka wajen inganta samar da kayayyaki a Nijeriya.
“Kamar misalin kamfanin Volkswagen da Peugeot, da kuma ma Toyota, za mu iya janyosu su kafa masana’antar hada Motocinsu a nan Nijeriya.”
Sanatar ta kara da cewa, sam bai kamata ba a shigo da wasu kayayyaki Nijeriya kamar irin su tumaturin gwangwani.