• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bai Kamata Japan Ta Zuba Ruwan Da Sinadarin Nukiliya Ya Gurbata Cikin Tekun Pasifik Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Japan

Ranar 22 ga wata, rana ce ta duniyarmu, wato “The World Earth Day” a Turance, kana rana ce ta doka ta duniya. Wasu kungiyoyi masu zaman kansu, da kungiyoyin kiyaye muhalli a duniya sun yi gangami, domin nuna adawa da shirin gwamnatin kasar Japan na zuba ruwan da sinadarin nukiliya ya gurbata daga Fukushima zuwa teku.

Ban da haka kuma, a kwanan baya, hukumar Greenpeace ta sossoki lamirin gwamnatin Japan kan shirin na ta, wanda ya saba wa yarjejeniyar dokokin teku ta MDD, da sauran dokokin kasa da kasa, hukumar ta kuma zargi gwamnatin Japan da gazawa wajen sauke nauyin kimanta illolin da shirinta zai haifar kan muhalli.

  • An Bude Bikin Fina-finai Na Kasa Da Kasa Na Beijing Karo Na 13

Cikin shekaru 2 da suka wuce, tun bayan da gwamnatin Japan ta sanar da shirin zuba ruwan da sinadarin nukiliya ya gurbata zuwa teku, ana ta bayyana adawa, da kuma nuna shakku kan shirin na Japan.

Amma gwamnatin Japan din ta kau da kai, tare da yin aniyar aiwatar da shirinta, duk da cewa har yanzu, hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA, ba ta kaddamar da rahoton ta na kimanta tasirin hakan ba.

Babban taken ranar duniyarmu a bana shi ne “Zuba kudi domin duniyarmu”. A shafinta na Internet, MDD ta yi kira ga kasashen duniya da su raya tattalin arziki mai dorewa. Zuba ruwan da sinadarin nukiliya ya gurbata cikin teku, ba zai shafi Japan kadai ba, domin kuwa hakan zai shafi daukacin bil Adama ne.

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Har ila yau tekun Pasifik, ba wuri ne da Japan za ta zuba shara ba ne, maimakon haka, teku ne da wasu kasashe suke dogaro da shi. Don haka kamata ya yi Japan ta daidaita ruwan ta hanyar da ta dace, bisa sanin ya kamata da kuma kimiyya.

Kafin dukkan sassa masu ruwa da tsaki sun tabbatar da cewa, shirin Japan ba zai haifar da illa ba, bai kamata Japan ta aiwatar da shirin na ta ba. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025
Next Post
Shawarar Kasar Sin Game Da Tsaron Kasa Da Kasa Ta Ingiza Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya, In Ji Masana

Shawarar Kasar Sin Game Da Tsaron Kasa Da Kasa Ta Ingiza Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya, In Ji Masana

LABARAI MASU NASABA

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025

Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.