Bakuwarmu Ta Yau: Hafsat Bauchi, Jarumar Fina-finan Hausa

Hafsat

A ci gaba da zakulo muku baki na musamman wanda suka shahara a bangaren wakoki da kuma fina-finai, a yau ma wannan shafin ya kara zakulo muku wata shahararriyar Jarumar wadda ta yi fice a masana’antar Kannywood wadda aka fi sani da Hafsat Bauchi, inda ta fayyacewa masu karatu tarihinta da kuma abubuwan da suka shafi sana’arta ta fim, ga kuma yadda hirar ta kasance.

 

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki…

Sunana Hafsat Ibrahim amma an fi kirana da hafsat bauchi, Ni dai haifar fiyar garin Bauchi ce na yi karatuna tun daga firamare har sakandare duk a garin Bauchi, inda na tsaya a matakin NCE. Ban ci gaba da karatu ba kuma bana aiki, amma ina da shop na sayar da dan wani kayan kyale-kyale na mata, yanzu haka ina masana’antar Kannywood.

 

Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Kawai sha’awa, Shi ne ya ja ra’ayi na.

 

Me ya fara baki tsoro game da harkar fim kafin ki shigeta?

Kawai ina jin kamar ba zan iya acting bane kamar zan yi ba dai-dai ba amma bayan nan babu wani tsoron da na ji.

 

Za ki kamar shekara nawa da fara fim?

Zan yi kamar shekara shida da farawa.

 

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?

Ni dai gaskiya ba zan ce na yi wata gwagwarmaya kafin na shiga ba, sai dai dan wasu da ba za’a rasa ba.

 

A wanne fim kika fara fitowa kuma wacce rawa kika taka a cikin fim din?

Na fara fitowa a Bazan sakeki ba, kuma ni ce na ja fim din. Rawar da na taka cikin fin din, Na fito ne wacce take da miji mai tsananin kishi mijin tsabar kishinsa duk namijin daya kalleni sai ya bishi gida ya kashe shi.

 

Ya kika ji lokacin da za ki fara fim din, Kasancewar shi ne farkon farawarki a lokacin?

Na ji kamar ba zan iya ba, amma kuma ina yin Sin daya sai na ji na sake na daina jin tsoron da nake ji.

 

Daga lokacin da kika fara fim kaho i-yanzu kin yi Fina-finai sun kai kamar guda nawa?

Gaskiya ba zan iya cewa nawa na yiba, tunda idan na yi ba wai ina kirgawa bane, amma ina ga ba zasu wuce 50 ba, Na yi product fim nawa na kaina ma guda 6.

 

Ko za ki iya fadowa masu karatu kadan daga ciki bayan wadanda kika fada dazu?

Ba zan sake kiba, Gaba da Gabanta, Ba iftila’i,  Nasibi, Gidan Narage, Farin Wata, Fuska Biyu,  Wacece, wanda zan iya tuna da sunansu kenan.

 

Na ji kin ce kin shirya fina-fina naki na kanki, ya sunan fina-finan kuma ya karbuwar fim din ta kasance?

A cikin fina-finan dana shirya biyu sun fita kasuwa, sauran kuma tukunna dai, fim dina Babban Zunubi ya karbu wajan jama’a sosai.

 

Cikin gaba daya fina-finan da kika fito wanne fim kika fi so kuma me yasa ki ke son sa?

Gaskiya ni duk fim din da zan fito ina sonsa.

 

Wanne rawa kika fi yawan takawa a fim?

Ko wanne ina takawa duk wanda aka bani ina koaarin ganin na yi abun yadda ya kamata.

 

Ko kina da iyayen gida a Kannywood, idan akwai su waye?

Akwai Abubakar S. Shehu, da kuma  Adam A Zango.

 

Su waye kawayenki a Kannywood?

Gaskiya ni bani da kawa amma dai ina mutunci da kowa.

 

Da wa kika fi so a hadaki a fim, kuma da wa kika fi yawan fitowa?

Ba ni da zabi a wannnan gaskiya ni duk wanda aka hadani da shi zan yi aiki.

 

Kasashe nawa kika taba zuwa ko gari nawa ta sanadiyyar fim?

Sanadiya fim kam na shiga wurare da yawa a Arewa kusan babu inda ban shigaba ba, kasa kuma na je Ghana Cameroon Niger duka wasan sallah sai Saudia na je na yi Umara.

 

Wanne irin nasarori kika samu game da harkar fim?

Na samu sanara kam wabda ba zan iya furtawa ba amma sai dai godiyar Allah.

 

Ko akwai wani kalubale wanda kika taba fuskanta game da harkar fim?

Gaskiya daga shigata har izuwa yanzu dai babu wani kalubale dana fuskanta game da fim.

 

Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin hakan wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba?

Ranar dana tsinci kaina a madina na ganni gani a kabarin Manzon Allah SAW na yi farin ciki mara misaltuwa. Na bakin ciki kuma ranar da aka kirani cikin dare aka ce shop dina na ci da wuta na shiga tashin hankali marar musaltuwa.

 

Me ki ke son cimma game da fim?

Fara fim da kudina kuma na fara toh na fara cimma burina.

 

Ya alakarki takeda sauran Jarumai?

Ina zaune lafiya da kowa dan banda abokin fada gaskiya.

 

Ya alakarki take ada da kuma yanzu da kawayenki da kuma irin lokacin da kike basu?

Akwai lokacin da nake warewa dan kaiwa kawayena ziyara ko su kawomin, saboda suna yawan korafin wai ina sharesu.

 

A baya kadan na ji kin ce kin bude wajen saida kaya,shin ke kike zama a shagon ko kuwa wasu kika diba su ke siyar miki, idan ke kike zama ta ya ki ke iya hada kasuwancinki da kuma sana’arki ta fim?

Gaskiya ba ni ce nake zama ba, amma akwai lokacin da nake zuwa na zauna saboda akwai wanda za su zo dan kaine. Fim yana da lokaci duk lokacin da na je aiki ina gamawa nake dawo bauchi.

 

Kafin ki shiga fim ko akwai wani ko wata da suke birgeki wajen yadda suke taka rawarsu, har ta kai da kema kina jin za ki rinka yin yadda suke yi?

Kowa yana burgeni musamman idan naga tana acting yadda ya kamata, amma ban taba jin wai na koyi abinda wata take yi ba gaskiya.

 

Kin shiga fim sabida kina sha’awar abin, shin a yanzu ya kika dauki harkar fim?

Na shiga fim a matakin ina sha’awar harkar, amma yanzu na dauke ta sana’a ce.

 

Kasancewar yanzu kin juma a cikin masana’antar kannywood, shin a  yanzu wacece ko wanene gwaninki?

Ni duk wanda zai yi abinda zai birge mutane shima gwanina ne ba ni da wabda zan zaba kowa na birgeni.

 

Me za ki ce game da irin mummunan kallon da ake yiwa ‘yan fim?

Wannan rashin fahinta ne yake kawo haka, baka san mutum ba baka taba ganin sa a zahiri ba, sai dai ka kalli fim dinsa amma za ka ji mutum yana yada labarin karya akansa, idan da za a tarke shi sai ka rasa ta ina maganar ta fara, ya kamata mutane su rinka yi mana adalci.

 

Yaushe za ki aure?

Yadda ba za ka san ranar mutuwar kaba haka ba za ka san yaushe za ka yi aure ba, amma kullum ina sama raina na kusa aure insha Allah.

 

Toh ya batun soyayya fa, shin ko akwai wanda ya taba kwanta miki a rai wanda har ta kai da kun fara soyayya da shi cikin masana’antar Kannywood?

Ban taba soyayya da kowa ba a cikin masana’antar kannywood.

 

Idan wani a cikin abokan aikinki na kannywood ya fito ya ce yana sonki zai aureki, shin za ki amince da aurensa ko kuwa ba kida ra’ayin hakan?

A shirye nake dana aureshi ai mutum baya tsallake kaddarasa, kamar yadda bai isa ya tsallake ajalinsa ba, kawai fatana Allah ya bani miji mai tsoron Allah.

 

Wanne irin Namiji kike son aura?

Gaskiya inason dogon namiji amma ba siriri ba jiant.

 

Idan kika ga ana kallon fim dinki wanne irin dadi kike ji cikin zuciyarki?

(Dariya), sai dai a kirani ace an gani, indai an gani gabana sai dai a gidan mu ake gani.

 

Ya ki ke da mutane wajen fita kamar in za ki unguwa ko makamancin hakan?

Idan ka fita dole sai dole ka hadu da mutane kam, amma babu yadda ka iya tunda kana abinda ka zama abin kallon wajan su. Idan zan fita ina sa nikab ne da, saboda idan ka fita ana kallonka nan sai duk ka tsargu kaima, wasu ma zuwa suke yi su ce sai kun yi photo ko akan hanya ne. Amma yanzu sai dai kasa facemask wasu duk da kasa sai ka ji sun kira sunanka, Ko kuma wani sunan da suka sanka a fim.

 

Wanne irin abinci kika fi so da abin sha?

Abinci ina son shinkafa da wake da mai da ya ji abinsha ina son fruit salad.

 

Wanne irin kaya kika fi son sakawa, kuma wanne kala kika fi so?

A gaskiya na fi son abaya dan yawancin kayana ma kenan na fi jin dadin sawa, color ina son jah.

 

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga fim da wadanda suke ciki?

Su zama mutanen kirki yadda duk inda za su shiga za su bawa mai kallo sha’awa.

 

Wanne kira za ki ga matasa marasa aikin yi?

Ina kira ga marasa aikin yi da su tashi su nemi na kansu, rashin aikin shi ne yake jefa matasan mu cikin halin kakanakayi.

 

Wanne kira za ki ga gwamnati musamman game da masana’antar kannywood?

Ban ma san me zan ce game da gwamnati ba, lokacin da ta yi yunkurin tallafa mana za ta yi fim billage aka hana saboda mutane basu ma fahinci menene ake nufi da fim billage ba, amma ai gwamnati kano tana iya kokarinta akan fim. Idan da gwamnati za ta waiwaiye mu, ta tallafa mana ai mun ji dadi ko saboda irin gudumawar da masana’antar kannywood take bata, Amma dun da hakan tana nata kokarin.

 

Me za ki ce da makaranta wannan shafin na Taskira?

Allah ya kara bunkasa ta, yasa mutane da yawa su amfana da ita.

 

Me za ki ce da ita kanta Jaridar Leadership A Yau?

Ina mata fatan nasara Allah ya kara daukaka jaridar leadership ya zama kowa na karanta ta.

 

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ina mika gaisuwata ga masoyana maza da mata ina musu fatan alkairi a koda yaushe.

 

Muna godiya Hajiya Hafsat

Nima na gode.

Exit mobile version