Bala’in Bazuwar Makamai A Nijeriya

A cikin wannan makon, sashen da ke kula da tabbatar da zaman lafiya da shawo kan matsalar da makamai a hannun jama’a ke haddasawa na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da hasken cewa akwai Makamai sama da milyan 350 a hannun jama’a da suka mallaka ba bisa ka’ida ba a Nijeriya.

Kididdigar sashen ya nuna cewa akwai makamai a hannun mutane sama da milyan 500 da ba su da rajista a fadin Afirka baki daya amma Nijeriya ce take da kashi 70 a cikin 100 na yawansu.

Sashen ya bayyana wannan lamarin mai matukar tayar da hankali ne a yayin gudanar da wani taron hadin gwiwa da ya shirya tare da Kwamitin Shugaban Kasan Nijeriya a kan shawo kan kananan makamai na yini guda a farkon makon nan.

An bayyana cewa hanyoyin da aka shigo da makaman su ne: imma dai ta barauniyar hanya ko kuma ta munafunci, wato yadda ake saka makaman a cikin wani abu domin bad da sawu kar a gane.

Ko a watan da ya gabata, rahotanni sun bayyana yadda jami’an tsaro na sirri suka yi zargin cewa wadanda ake dauka aiki a hukumomin da suka shafi tsaron kasa ke sayar da makamai ga bata-gari da sauran mutanen da ba su dace ba. Hukumar ta ce wannan kari ne a kan matsalar daukar matsafa, ‘yan fashi da makami da sauran bata-gari aiki a cikin hukumomin tsaron har da rundunonin soja.

Wannan bai zo wa al’umma da mamaki ba saboda yadda Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa (Kwastam) ta rika damke tarin makamai a manyan tashoshin gabar ruwa da aka kuduri aniyar shigo da su kasar nan.

Wannan babban abin yabawa ne ga hukumar a zahiri, amma kuma bisa wani kishin-kishin da muka ji daga wata majiya a hukumar, akwai lauje cikin nadi kan yadda aka rika cafke makaman cikin nasara.

Majiyar ta ce babu wani abin birgewa game da kamen makaman, domin zai iya yiwuwa mai shigo da makaman ‘bai ba su nagoro mai kauri ba ne’, wanda yake nufin jami’an sun tona asirin shigo da makaman ne saboda ba a ba su cinhanci mai tsoka ba. Ma’ana dai, da mai shigo da makaman ya ba su cinhancin, haka za a silale a shigo da makaman cikin kasar nan. Galibin ‘Yan Nijeriya sun yi amanna da cewa ana baiwa jami’an tsaro kudin nagoro su rika bari ana shigo da abin da zai cutar da Nijeriya da al’ummarta, amma muna fata Allah ya sa hasashe ne kawai ba da gaske ba.

Bazuwar makamai a kasar nan ta dade tana ci wa al’umma tuwo a kwarya saboda bala’o’in da hakan ke jawowa. Abin har ya kai ga sau tari jami’an tsaro ba su iya fuskantar bata-garin da ke ta’asa da wadannan makaman. Za su fita walau da rana ko dare suna cin karensu babu babbaka tamkar wasu da iyayensu suka aike su yi.

Idan ba a manta ba, a kwanan baya lokacin da sace-sacen jama’a da fashi da makami suka yi mugun kamari a manyan hanyoyin kasar nan, sai da babban sufetan ‘yansanda da kansa ya tarwatsa shingayen ‘yansanda da ke kan titunan tare da kawo wasu sabbin jami’ai su maye gurbin daukacin wadanda suke bakin aiki a lokacin. Ba wai babban sufetan ya yi wa ‘yansandan da ke bakin aikin mugun shaida ba ne, amma dai ‘Yan Nijeriya sun san cewa jami’an sun gaza yin katabus ne a bakin aikinsu. Tabbas kuwa, maye gurbinsu ke da wuya aka fara damko gagga-gaggan masu aikata miyagun laifukan a hanyoyin wanda lamarin ya yi sauki yanzu.

Bala’in shigo da makamai babu wanda zai ce ga irin ta’asar da zai iya haifarwa. Shi ne ummul’haba’isin tabarbarewar tsaro. Shi ne sanadin salwantar da rayukan wadanda basu-ji-ba-basu-ga ba. Shi ne silar rashin kwanciyar hankali da walwalar jama’a kamar yadda jama’a ke dandana kudarsu a hannun masu satar mutane, fashi da makami. Shi ne kanwa uwar-gamin karya tattalin arziki kamar yadda aka shaida lokacin da tsagerun Neja Delta suka kaddamar da hare-haren barnata bututun mai. Bala’in ne yake ruru wutar rikicin kabilanci kamar yadda suka sha faruwa a lokuta daban-daban a kuma sassa mabanbanta na kasar nan. Illolin abin ba za su kidayu ba.

Duk da gwamnati tana bakin kokarinta kamar yadda take nunawa a zahiri game da shawo kan matsalar, amma ya kamata ta san da cewa samar da dokoki masu inganci ba za su wadatar ba, dole sai an jajirce tare da mayar da hankali wurin aiwatar da dokokin.

Sannan a tabbatar da tsarkin duk wadanda za a damka wa alhakin abin domin kauce wa haihuwar uwar guzuma, da-kwance-uwa-kwance!

Exit mobile version