Dan wasan tsakiyar Manchester City kuma dan kasar Spain, Rodrigo Hernandez ya mayar da martani ga Cristiano Ronaldo kan ikirarin da ya yi cewa, Rodri bai cancanci lashe kyautar ba a bana.
Ronaldo a wani bikin bayar da kyaututtuka da ya halarta a London ya yi tsokaci dangane da kyautar da dan wasan Manchester City ya lashe inda yace, Vinicius JR. na Real Madrid ya cancanci lashe kyautar ba Rodri ba.
- Ɓaraka:, Ƴan Adawa, Shugabannin APC Na Shirya Kafa Sabuwar Tafiya — Lukman
- Gwamnatin Kano Ta Yi Fatali Da Kudirin Sake Fasalin Dokar Haraji
Hakan yasa yanzu kuma Rodri yace duk da cewar Cristiano Ronaldo bai goyi bayan lashe kyautar Ballon D’or na bana da yayi ba, amma kar ya manta cewar, yan jarida da sauran manyan mutane da suka zabi Ronaldo har ya lashe kyautar a baya su ne suka zabe shi yanzu.
Ronaldo ya lashe kyautar Ballon D’or sau biyar a tarihi, sai Messi wanda ya lashe kyautar har sau 8, wanda shi ne ne kadai dan wasan da yafi Ronaldo lashe kyautar a tarihi.