ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ban Dogara Da Harkar Fim Shi Kadai A Rayuwata Ba — Maryam Usman(2)

by Rabi'at Sidi Bala
18 hours ago
Fim

Shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jarumai manya da kanana daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood, kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wata fitacciyar jarumar wacce ta shafe tsahon shekaru a cikin masana’antar Kannywood wato, HAJ. MARYAM USMAN wacce aka fi sani da ANTI MA Inda ta bayyanawa masu karatu irin matsalolin da ake fuskanta a cikin masana’antar Kannywood, kana Jarumar ta yi bayani game da abin da ya shafi rayuwarta da kuma sana’ar ta. Baya ga haka jarumar ta bayar da shawarwari ga masu kokarin shiga harkar fim, har ma da wasu batutuwan masu yawa.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

  • An Bukaci Amurka Da Ta Kauracewa Sanya Wasu Sassa Na Muzgunawa Kasar Sin Cikin Kudurin Dokar Tsaron Kasa
  • GORON JUMA’A

Wadanne irin tambayoyi ake yi miki da zarar an ci karo da ke a zahiri?

ADVERTISEMENT

A fim ina da zafi amma wani ikon Allah duk wanda ya ganni a waje sai ya ce “daman haka ki ke, kina da kirki da fara’a?”, wallahi mutuniyar kirki ake daukata, iya wannan matar da ta zagen ce kadai ta dauken da wata fahimta, saboda fara’a ta, ta yi yawa ita take ragen zafin nan na fim ake ganin kirki na, amma kuma ina da kirkin.

 

LABARAI MASU NASABA

Na Ɗauki Harkar Fim Tamkar Aikin Gwamnati — Maryam Usman

Tun Ina Yarinya Sana’ar Fim Ke Burge Ni —Hafsat Salisu

A cikin shirin Garwashi kin fito a uwar da ta takurawa ‘yarta wajen fito da miji tamkar ba ke ki ka haife ta ba, shin ya ki ka ji a wannan rawar da ki ka taka, shin za ki iya yin hakan a gaske?

Ai wannan fim ne idan na yi haka a zahiri na ja da ikon Allah, ko ni ‘ya ta bata yi aure ba ta tafi bautar kasa, to, sai na takura mata na ce sai ta yi aure?, kawai a Garwashi rol ne. Kuma wallahi duk fadan nan da nake yi mata hankalina yana tashi, saboda wannan ‘yar babanta ubangidana ne a ‘History and Culture’, ina jin zafi idan ina yi mata fadan. Amma da yake duniya suna kallon mu da akwai iyaye masu yin haka shi ne nake yi. Amma ba na jin dadi nake yi mata.

 

Ko kina da ubangida a cikin masana’antar Kannywood?

Duk wanda ba shi da ubangida ko a bariki ne ya yi asara bare kuma a harkar neman abinci, ina da iyayen gida da yawa masu albarka, masu sanin ya kamata, wanda in Allah ya yarda indai an yi duniya dan Annabi Muhammadu (s.a.w) sai sun gama da duniya lafiya. Kuma ina fatan Allah ubangiji ya bude musu kofofin samu gabas da yamma, kudu da arewa, ya toshe musu kofar rashi ya dora su akan makiyinsu. Duk wanda baya son su Allah yayi gaba da shi uwa kirji.

 

Mene ne burinki na gaba game da fim?

In gama da duniyar fim lafiya, kar in zamanto me yi wa ‘yan’uwana sharri ina bata musu suna, ko ina yi musu hassada, ko ina so a kuro su su shiga wahala, Allah ya dafawa ‘industry’ manyan mu da kanana, Allah ya yi mana albarka gabadayanmu. Sannan burina na biyu shi ne; Ina so na kara zama wata a duniyar ‘Industry’ nake taimako; asibiti, marayu, matan da ba su da mazaje, da wasu abubuwan masu albarka nake so na yi. A haka ma ina yi daidai karfina, amma Allah ya karo min, ina so na gama da fim lafiya, saboda fim ya min riga ya min wando, ya min zanin yafawa har da takalma da ‘yan kunne da sarka.

 

Ko akwai wani fim wanda ki ka fito cikinsa, daga baya ki ka yi da-kin-sanin fitowa cikinsa?

[Dariya] Allah sarki, haka na rika cika baki ina cewa kowane fim zan yi a duniya amma ban da kwartonci, da na ga dai da gaske a zahiri ba kwartuwar ba ce kuma fim ne ana kwatantawa ne, wallahi sai da na fito a kwartuwa cikin Allura Cikin Ruwa. Kuma masu so na suka yi ta fada wai ban kyauta ba da na yi haka, na ce musu fim.ne. suka fahimce ni kuma suka yi min kyaututtuka da dama. Har yau ban taba yin fim din da na yi da-na-sani ba, kuma na san ba zan yi ba. Saboda duk rol din da ki ka ba ni zan yi, ko ke yanzu ki ke so ki yi fim ko a barauniya ki ka saka ni, zan fito.

 

Wane fim ne ya taba faranta miki ko bakanta miki, kuma me ya sa?

Wallahi ni dai har yanzu ko dan ‘yar fari ce ban sani ba, amma babu fim din da ya taba bata min rai. Saboda idan aka saka ni fim da gaske nake yin su, a fim din ma wani abun wanda ya faru da ni ne, wani kuma abin da ya faru da dan’uwana ko ‘yar’uwata. Fim daya ne hankalina ya tashi wai shi ‘Rikici’, muna cikin fim din wata mahaifiyar mu ta rasu, shi ne kawai bacin raina, sai daga baya na ga mutuwar nan dole ce,

 

Ko akwai wasu matsaloli a cikin masana’antar Kannywood wadanda ki ke ganin ya kamata a gyara su?

Akwai matsaloli, yadda ‘yan’uwanmu suke burmawa cikinsu wuka, suke tonawa ‘yan’uwansu asiri saboda a tsane su, ni abin da yake damuna kenan. Ni kin ga ana yawan ce mana gabadayanmu karuwai ne, bai taba damuna ba saboda ba karuwan bane. Kuma ko a Saudiya da akwai karuwai to, duk wanda zai yi karuwanci zai yi, wanda zai yi fim zai yi. Sannan da wadanda suke zuwa su sayi ‘form’ din fim a tunaninsu yanzu-yanzu za su samu mota ko gida ko kudi. Ba su san wuyar da mutum ya sha ya samo ba, sai su janyo a yi ta zaginmu su suke bata min rai, kuma in Allah ya yarda za a gyara. Allah ya shirye mu gabadayanmu babu wanda ya fi karfin kaddara.

 

Misali ki zama shugaba, wane irin cigaba ki ke ganin za ki kawo ga masana’antar Kannywood?

Dole karami ya bawa babba girmansa, kuma duk wanda ya san yana bata harkar fim rayuwar kurkuku zai yi. Saboda fim sana’a ce babba a duniya, ko indiya da kudin fim suka yi arziki a garinsu. Sannan ‘yan ‘Nigerian film’ din nan su ma suna fim amma kina ji suna batawa ‘yan’uwansu suna kamar mu? Hassadarsu tana fitowa fili kamar mu?, suna kin ‘yan’uwansu kamar mu?. Kananan yara-yaran nan da suke bata rayuwarsu da son duniya yanzu-yanzu sai na zama wasu to, su ne za mu debo malamai nasa a rika yi musu nasiha har sai hankalinsu ya dawo jikinsu. Arziki fa na Allah ne, in bai ga dama ka yi ba, wallahi baka isa ba ko uwarka bata isa ta saka ka ba. Idan kuwa ya ga dama ko ubanka ne beran masallaci wajen talauci sai ka zama wani a duniya. In Allah ya so sai ya mayar da Gertai sarki, in kuma ya so yanzu-yanzun nan shugaban kasa sai ya zama Shushaina.

 

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Ni da nake da ‘ya’ya na halak a karkashina da ‘ya’yan ‘yan’uwa wadanda iyayensu suka mutu, ai dole na yi sana’a, ba zan dogara da fim shi kadai ba.

 

Ya alakarki take da sauran jarumai, da kuma wadanda ku ke tare da su tun kafin ki fara fim?

Ni da yake bana manta baya hatta kawayena da mukai firamare da sakandare har yanzu ina tare da su, duk wanda dai mukai makaranta muna tare. Wanda suka mutu su ne ba na tare da su, amma ina tare da ‘ya’yansu, da iyayensu. Sannan ‘yan cikin Kannywood ina da alaka kyakkyawa da su, saboda bana fada da kowa. Fada na kawai a iya fim ne, amma a waje in za a raina min hankali tijarata ta fi ta cikin fim din, sai na tabbatar na karbowa kaina ‘yanci, saboda ni a duniya ba abin da na sani irin ‘women right’ dina.

 

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shigowa harkar fim?

Ina yi musu farinciki da shigowa amma su shigo da zubiya me kyau, saboda ni har yau a duniyar fim ban ga malamin da yake koya badala ba, ban ga malamin da yake koya rashin hankali ba, amma na ga malamin da yake koya tarbiyya a fim. To, su shigo wurin malaman da suke koya tarbiyyar nan, kar su shigo da son duniya. Saboda son duniya sai Allah ya yi, idan Allah bai yi a fim za ki yi arziki ba, ba za ki yi ba. In kuma Allah ya yi a fim za ki yi arziki to za ki yi. Kar ki shigo da son yanzu-yanzu idan na shigo anjima zan yi mota, ki bi a hankali. Dan ni har yanzu ban hango makusarsa ba, da babata tana raye ta ce za ta shigo fim barinta zan yi. Haka ‘ya’yana duk wanda ya ce zai yi barinsa zan yi.

 

Ko akwai wata shawara da za ki bawa sauran abokan sana’arki na fim?

Shawara ta wuce dan’uwanka ya daina yi wa dan’uwansa hassada ko ya daina bakin ciki da abin da dan’uwansa ya samu, ko mu daina kushe da hassada, mu daina tsanar ‘yan’uwanmu a aikin banza, mu zauna lafiya mu hada kai dan mu kai gaci.

 

Me za ki ce da gidan jaridar Leadership Hausa, har ma da masu karanta wannan hirar taki?

Ina yi wa gidan jaridar LEADERSHIP HAUSA fatan alkhairi me dimbun yawa, ke da ki ka bata lokacinki ki ka yi hira da ni Allah ubangiji ya yi miki albishir da gidan aljannah. Allah ubangiji ya daukaka wannan gidan jarida gabadai-gabadai. Duk wanda yake aiki a gidan jaridar nan Allah ubangiji yayi masa abin da zai yi masa na alkhairi. Ina gaishe ku gabadayanku ina kaunarku, ina yi muku fatan alkhairi na gode, wannan hirar ma daukaka ce. Daga karshe ina yi wa aminiyata kawata Haj. Adaman Kamaye godiya da fatan alkhairi a gare ta, Na gode Allah ya bar zumunci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fim
Nishadi

Na Ɗauki Harkar Fim Tamkar Aikin Gwamnati — Maryam Usman

December 14, 2025
Tun Ina Yarinya Sana’ar Fim Ke Burge Ni —Hafsat Salisu
Nishadi

Tun Ina Yarinya Sana’ar Fim Ke Burge Ni —Hafsat Salisu

November 30, 2025
Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA
Nishadi

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025
Next Post
An Yi Bikin Cika Shekaru 26 Da Dawowar Yankin Macao Kasar Sin

An Yi Bikin Cika Shekaru 26 Da Dawowar Yankin Macao Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.