Tsohon shugaban kasar Nijeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Bababangida, ya karyata rahotannin da wasu kafafen sada zumunta suka wallafa cewar ya goyi bayan takarar Peter Obi, na jam’iyyar LP a zaben 2023.
A wata kafa ta wallafa cewar IBB, ya ayyana goyon bayansa ga Obi kamar yadda tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi ga dan takarar.
- Zan Yi Wa Kowa Adalci Idan Na Ci Zabe – Tinubu
- Tashar Jiragen Ruwa Ta Shanghai Ta Kasance Mafi Hada-Hadar Kwantenoni A Duniya A 2022
IBB, ya karyata hakan ne ta hannun mai magana da yawunsa, Prince Kassim Afegbua, inda ya ce, mai gidansa IBB bai fitar da wata sanarwa a kan goyon bayan takarar Peter Obi ba.
Kassim ya kara da cewa, tsohon shugaban kasar bai da wani shafi a Twitter.
Ya bayyana cewa, wannan labarin na kanzon kurege ne, inda kuma ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton domin bai da wani tushe ballantana makama.
Ya sanar da cewa, idan har mai gidansa zai yi wata magana, yana fitar da sanarwa ne ba ta kafafen sada zumunta ba.