Ado Aleiro, dan bindigar da ya addabi jihar Zamfara da Katsina, wanda aka nada a matsayin Sarkin Fulani a Zamfara, ya ce babu wanda ya nema don yi masa sarautar.
Aleiro ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da DW Hausa kuma ta wallafa a ranar Lahadi.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Sace Matafiya Da Dama A Katsina
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Mahara 2 A Anambra, Sun Kwato Makamai
A ranar 16 ga watan Yuli ne Sarkin Yandoto, Aliyu Marafa, ya nada Aleiro a matsayin Sarkin Fulani a karamar hukumar Tsafe ta jihar.
Sai dai rundunar ‘yan sanda ta ce Aleiro na cikin jerin sunayen kasurguman da ake nema ruwa a jallo bisa zarginsa da hannu ra cikin ayyukan ‘yan bindiga.
Nadin sarauta ya janyo takadda sosai, hakan ya sa gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya dakatar da sarkin ‘Yantodo saboda bai wa Aleiro sarauta.
Matawalle ya kuma haramta wa sarakunan gargajiya a jihar bayar da mukaman sarauta ba tare da samun amincewar gwamnatin jihar ba.
Da yake mayar da martani kan nadin sarautar, Aleiro, ya ce masarautar ce ta neme shi da kanta.
“Bari in fada muku gaskiya, ba ni na nema ba; su suka neme ni game da hakan,” in ji Aleiro.
“Sun yi waya sun sanar da ni abin da za su ba ni. Sai na ce ‘a’a, wannan bai kamata ya faru ba.
“Amma da yake ina da iyaye, daga baya muka zauna muka tattauna a kai, kuma tun da sabon sarki ya fadi abin da yake son yi a masarautarsa, sai na amince.”
Ya kuma musanta cewa yana da hannu a wani harin da aka danganta da shi a kauyen Kadisau da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, wanda ya faru a watan Yuni kuma aka kashe sama da mutane 30.
“Maganar Kadisau, don Allah, ina rokonka da sunan Allah da ka tambayi Sarkin Kadisau ko kuma ka nemi lambarsa ka tambaye shi musabbabin harin,” in ji shi.
“An yanka ‘yan uwanmu ne a cikin wani masallaci a ranar Juma’a a garin Kadisau. Abin da ya jawo harin kuma ‘yan uwansu ne suka dauki fansa. Ban san lokacin da harin ya faru ba; amma an alakanta ni da harin.”