Dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC a Jihar Yobe ta Arewa, Bashir Machina, ya ce bai yi nadamar kare hakkin al’ummar yankinsa a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Machina, ya bayyana haka ne ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Husaini Mohammed Isa, a lokacin da yake jawabi ga daruruwan magoya bayansa a kananan hukumomin Karasuwa da Yusufari.
- Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa – MDD
- Fitacciyar Mawakiya Ta Jamhuriyar Nijar Hamsou Garba Ta Rasu
“Ina ganin wannan wata babbar dama ce da ba kasafai ba na yi wa mutanen Yobe ta Arewa hidima kuma babban abin godiya shi ne samar da ingantacciyar hidima da jagoranci mai ma’ana wanda zai daukaka martabar yankinmu na majalisar dattawa,” in ji shi.
Ya kara da cewa ba ya jin haushin wadanda suka yi masa hadaka, inda ya ce ya ajiye duk abin da ya faru, don haka ya bukaci magoya bayansa da su yi hakan.
“Na yafe wa wadanda suka yi min hadaka, abin da jam’iyyar APC a jihar ke bukata a yanzu shi ne duk masu ruwa da tsaki su hadu domin ciyar jam’iyyar gaba”, in ji Machina.
Yayin da yake a fadar Sarkin Yusufari, dan takarar Sanatan ya tabbatar wa Sarkin cewa ba zai taba bai wa al’ummarsa kunya ba.
Idan za a tuna cewa Machina ya samu nasara a shari’ar da kotu ta yi wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kan tikitin takarar Sanatan Yobe ta Arewa.