Connect with us

SIYASA

Ban Turo Kowa Yayi Takara Ba- Lolo

Published

on

Gwamnan Neja Dakta Abubakar Sani Bello ya nisanta kan shi da jita-jitar da ake yadawa na turo wasu yin takaran kujerun majalisar dattijai, wakilai da na jahohi a siyasar 2019 mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani kwarya-kwaryan taron da ya kira zababbun wakilai da sanatoci da ‘yan majalisun jiha da shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a jihar a daren asabar din makon nan, inda ya bayyana cewar ‘ Shi bai da wani dan takara da ya turo da sunan ya je yayi takara domin kowa na shi ne, idan kana sha’awar takarar kowani kujera kaje ka nemi hadin kan jam’iyya da al’ummar da za ka shugabanta.
Majiyar Leadership Ayau ta tabbatar da cewar lamarin ya taso ne inda wasu na gindin gwamnan ke kokarin anfani da kusancin su da gwamnan na ganin sun kakabawa jama’a ‘yan takara ta yadda zasu cigaba da cin karensu ba babbaka.
Tun kafin wannan lokacin dai ana ta yada jita jita da farfagandar cewar wasu ‘yan takarar na 2019 gwamna ne ya turo su da zummar suyi takara a zabe mai zuwa, musamman wadanda ke da kusanci da gwamnan hakan ya yi ta haifar da rudani a tsakanin magoyabayan ‘yan takarkarun da ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar ta Neja.
Wani jigo a jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunansa, yace wannan matakin na gwamna abin ayaba ne domin akwai masu kokarin ganin indai ba su samu sai dai a fasa kowa ya rasa kuma majibintan gwamnan ne da wasu shugabannin jam’iyya a jiha. Ya kamata kamar yadda gwamna ya nisanta kansa da wadannan ‘yan takarar da ke kokarin shiga lemarsa dan biyan bukatarsu su sani ita siyasa hikima ce da iya tafiya da mutane, mun baro siyasar banga da babakere in har suna bukatar taimakawa gwamnan ne to lallai su tsaya tsayin daka wajen tallata ayyukan da gwamnan ya yiwa jama’a ba kokarin kawo rarrabuwan kawuna ba, ita kanta jam’iyya tana da rawar takawa, domin 2019 da muke gani ba irin 2015 ba ne da ya gabata, a bayan guguwar Buhari ta baiwa jama’a da dama kafa, amma yanzu koda a APC ka ke indai ba kai aikin komai ga al’umma ba kar ka yi tsammanin samun galabar zabe.
Dan haka ina jawo hankalin magoya bayan gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello da jam’iyyar APC da mu tashi tsaye wajen isar da sako ga jama’a, mu nuna masu ayyukan da gwamnati tayi, mu nuna masu alfanun sa ke ba shi dama karo na biyu yafi muhimmanci akan neman takara da karfin tsiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: